1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kotu ta tabbatar da nasarar Bola Ahmed Tinubu

Uwais Abubakar Idris AH
October 26, 2023

Alakalai bakwai na kotun kolin Najeriyar karkashin mai shari’a John Inyang Okoro ne suka yanke hukunci a kan karara da ‘yan takarar jam'iyyun biyu suka shigara a gabanta.

Nigeria | Bola Tinubu
Hoto: Sunday Aghaeze/Nigeria State House via AP/picture alliance

Daya bayan daya mai shari’a John Okoro ya rinka karanta karar yana watsi da ita a bisa tanajin da ya ce na shari’a ne bisa ga tsarin mulkin Najeriya. Kama daga batun zargin shugaban Najeriyar ya gabatar da takardu na jabbu na kammala jami’arsa abin da kotun ta ce sun makaro a kan wannan batu, ya zuwa batun gaza aikawa da sakamakon zabe ta yanar gizo shi ma kotun ta ce wannan bai shafi hallacin zaben ba. Har zuwa shaidu da suka gabatar na suka ce an tafka magudi, shi ma kotun ta ce tunda su wakilan zaben ne to runfarsu ce kawai za su iya ba da shaida.Duk da daukan hankalin da shari’ar ta yi mutanen da suka samu shiga kotun ba su da yawa saboda matakan tsaron da aka dauka, inda aka baza jami’ai a tituna har zuwa ga haraba da ma cikin kotun. Domin hatta abokan aikinmu sun sha artabukafin wasunmu muka samu shiga.

Kotu ta rab a gardama a kan batun zaben Najeriya da ake yin ja-iin-ja

Hoto: Kola Sulaimon/AFP/Getty Images

A yanzu dai an kawo karshen wannan batu kenan, domin daga wannan kotun to sai a dangana, wadanda suka samu nasara su ci gaba da mulki saura kuma su fara shirin wani zabe a shekara ta 2027.