1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Najeriya: Kungiyar malamai NUT ta kira yajin aiki

Abdullahi Tanko Bala
June 1, 2026

Kungiyar malaman Firamare da Sakandare ta kasa a Najeriya NUT ta kira yajin aiki daga wannan Litinin domin nuna bacin rai da sace dalibai da malamansu a Jihar Oyo

Nigeria Papiri 2025 | Klassenzimmer der St. Mary's Schule nach Massenentführung
Hoto: Ifeanyi Immanuel Bakwenye/AFP

A ranar 15 ga watan Mayu ne dai yan bindiga wadanda sojojin Najeriya suka zarga da cewa mayakan Jihadi ne na Boko Haram suka sace dalibai a makarantu uku a kudu maso yammacin Jihar Oyo.

Sun yi awon gaba da malamai bakwai tare da yara tsakanin 25 zuwa 39 yan shekaru biyu zuwa 16 a cewar Jami'ai. Har yanzu ana ci gaba da neman su.

Kungiyar malaman Firamaren da sakandare ta jihar Oyo ta ce ta dakatar da dukkan ayyuka a makarantu daga wannan Litinin har sai illa ma sha Allahu.