1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kungiyar PENGASSAN ta janye yajin aiki a Najeriya

Abdoulaye Mamane Amadou
October 1, 2025

Bayan bore da yajin aiki na tsawon kwanaki biyu, kungiyar ma'aikatan man fetur ta kasa PENGASSAN ta janye yajin aiki a Najeriya

'Yan Najeriya na farautar man fetur saboda karancin mai
'Yan Najeriya na farautar man fetur saboda karancin maiHoto: Sunday Alamba/AP/picture alliance

Kungiyar ma'aikatan man fetur da iskar gas a Najeriya PENGASSEN ta sanar da janye  yajin aikin da ta yi na kwanaki na biyu a Najeriya, bayan shiga tsakanin da jami'an gwamnatin kasar suka yi kan rikicin kungiyar da matatar mai ta Dangote.

Kungiyar PENGASSAN ta shiga yajin aiki

Ministan kwadagon Najeriya Dr Mohammed Maigari Dingyadi ne ya sanar da janye yajin aikin a cikin wata sanarwar da ya fitar a wannan Laraba, inda ya sanar da cewa matatar Dangote ta amince ta dawo da ma'aikata 800 da ta kora saboda sun shiga kungiyar ma'aikata, su kuma jami'an kungiyar za su fara komawa bakin aiki.

Festus Osifo shugaban kungiyar ma'aikata ta PENGASSAN a Najeriya ya ce duk da amincewa su janye yajin aiki batun yancin ma'aikaci ya shiga kungiyar ma'aikata abu ne na daban da tsarin mulkin Najeriya ya mallaka wa ma'aikaci.

"Ya ce mutane sun cika bisa radin kansu ne suka yanke hukuncin shiga kungiyar Pengassan ba tare da shamaki ba, sun cika takardun shiga kungiyar wannan kuma bisa hurumin sashi na 40 na kundin tsarin mulkin Najeriya da ya bada ‘yancin haka."

Najeriya: Hakar mai a Ogoni zai taimka?

A ranar 29 ga watan Satumba da yagabata ne aka kaddamar da taro don slhunta rikicin matatar man Dangote da kungiyar ta PENGASSAN wanda gwamnatin Najeriya ta jagoranta, kuma ta sanar da amincewar bangarorin biyu.