1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Najeriya: Kura ta lafa bayan hari a Gwaska

May 7, 2018

Mutane 45 zuwa 50 da suka hada da mata da yara kanana ne suka halaka a harin da wasu 'yan bindiga suka kai a kauyen Gwaska na karamar hukumar Birnin Gwari a jihar Kaduna.

Kamerun Anschlag in Maroua
Hoto: Getty Images/AFP/Stringer

 A ranar Asabar da ta gabata ce, ‘yan bindiga suka kai harin a kauyen na Gwaska inda suka halaka mutane da dama da suka hada da mata da kananan yara da tsofaffi da kuma dai wasu ‘yan sintiri masu sa kai da ke kare garin.

Tuni dai aka yi jana’iazar mutanen da yammacin lahadi. Sai dai kuma har ya zuwa wannan lokaci wasu mutanen mazauna wannan kauye na cikin dokar daji ba a san inda suke ba. Malam Awalu Sani mazaunin kauyen Birnin Gwarin Kaduna ya bayyana cewa maharan su kimanin dubu ne a saman baburra suka kawo wannan farmaki a garin da kimanin karfe biyu da rabi na rana.

Awalu ya ce abun na farko da suka yi shi ne zagaye garin da kuma hana kowa shiga ko tunanin ficewa daga cikin wannan gari. Daga nan suka buda wuta a kan mutanen kauyen inda babu abin da mutun ke ji illa karan bindigogi da iface-ifacen mutanen da ake kisa da wadanda ke neman gudu. Kuma ya ce mata da kananan yara tare da tsaffin sune lamarin ya fi rutsawa da su: 

“ Mun kirga mutane da yawa da suka mutu a sanadiyya wannan sabon farmaki, kuma ina mai tabbatar maka da cewa wadannan matane ne da aka koro su daga wasu jihohijn da ke makwabtakla da Kaduna,da suka yada zango kuma daga cikinsu akwai mayakan Boko Haram da wasu mutane da ba a san daga ko ina ne suka fi fito ba"

Mazauna kauyen dai sun nunar da cewa maharan da suka kawo wannan hari a kan Babura ne suka zo dauke da manyan makamai, kuma suna da yawan gaske inda suka kona gidaje masu yawa. 
 
Sai dai a sakamakon wannan tashin hankali ana samin sabanin addadin yawan mutanen da suka halaka, domin kowa shuwagabannin al'ummar garin Gwaska na cewa an hallaka masu mutane sama da 50. Sai dai rudunar ‘yan sandar jahar Kaduna  ta shaida wa manema labarai cewa mutun 45 ne aka tabbatar da mutuwarsu.

Hoto: picture-alliance/dpa

Kwamishinan 'yan sanda na jahar Kaduna Austin Iwar, ya ce suna da labara rasuwar mutane 45, kuma rundunar na kokarin ganin an kawo karshen wadannan tashe-tashen hankula 
A wata ganawar da tashar DW ya nunar da cewa suna tattaunawa da dukkanin masu ruwa da tsaki a harkar tsaro ga mazauna wannan yanki, kuma suna bukatar hadin kai daga al'umma domin dakile ci-gaban wadannan hare-hare.

Malam Mohammed Abubakar wani mazaunin kauyen Birnin Gwari da ke bayyana garuruwan da mahara yanzu haka suka mamaye wadanda aka korosu daga wasu jihohin makwabta da ke zaune a cikin dajin Birnin Gwari:

Hoto: Reuters

” Ina mai tabbatar maka da cewa akwai garuruwa kusan 30 da ke karkashin wadannan mutane, su ne ke mulkan wadannan garuruwa, kuma sun dade suna gudanar da abun da suke gudanarwa ba tare da fuskantar wata matsalar ba. Muna rokon mutanen gari da su taimaka mana da addu’o'i kan wannan iftila’i da ya same mu. Tun kwanakin baya mun yi ta ganin wasu jiragen sama suna sauka a cikin wadannan dazuzzuka, mun yi ta kai rahotanni ga jami’an tsaro anmma babu wani matakin da hukumomi  suka dauka"

Abubakar ya ce garuruwan irin su Gwauran Dutse da yankin magajin gari 3, yankin Kwadaga da Ci-Bauna da sauran garuruwa masu yawan gaske suna karkarshin ikon wadannan mutane
A tsakanin mako daya, mutane sama da 70 ne suka halaka a birnin Gwari. Idan kuma ba a manta ba a makwan da ya gabata ne shugaban ‘yan sandan Najeriya ya bayar da umurnin aikawa da 'yan sanda 200 domin kawo zaman lafiya a garin birnin gwari.