Ra'ayoyi mabambanta kan gyaran dokar 'yan sanda
December 6, 2018A Najeriya ra'ayoyi sun sha bambanta a kan kokarin yi wa shirin dokar aikin 'yan sanda gyaran fuska musamman a kan ikon da majalisar dokokin kasar ke son ta samu na amincewa da wanda za a nada sifeto janar na 'yan sandan Najeriyar, abin da wasu ke kalon cusa siyasa a harkar tsaro ba zai yi wa kasar kyawo ba.
Wannan aiki na yi wa dokar 'yan sandan gyaran fuska domin samar da sabuwa ta wannan shekara da majalisar dattawa ke yi, wani yunkuri ne na kyautatawa da ma inganta tsarin aikin 'yan sanda a kasar, biyo bayan damuwa na rashin tasirin aikin nasu wanda saboda sukurkucewarsa a 'yan shekarun nan mafi yawa sojoji ake gani suna aikin 'yan sanda a tsari na dimukuradiyya.
To sai dai batun bai wa majalisar ikon nada sifeto janar na 'yan sanda da a yanzu yake ikon shugaban Najeriya ne ya dauki hankali sosai a wajen wannan taro da ya sanya sifeto janar na 'yan sandan Ibrahim Idris bayyana adawarsa a fili bisa tsoron jefa siyasa cikin lamarin yana mai cewa.
"Rundunar 'yan sanda na da tunanin cewa a ce sai majalisa ta amince da sifeto janar kafin a nada shi zai ba da kafa ta cusa siyasa a lamarin, zai kawo cikas ga kokarin 'yan sanda na yakar masu aikata miyagun laifuffuka."
Akwai dai masana a harkar tsaro da tsofafin jami'an 'yan sanda da su ma suka tofa albarkacin bakinsu.
Ana dai wannan kokari bayan yi wa 'yan sandan karin albashi. Kwararru na bayyana yi wa daukacin tsarin garambawul kama daga yakar cin hanci da ya yi katutu a cikinsa da ma kara yawan 'yan sandan Najeriyar daga sama da dubu dari uku a kasa mai yawan jama'a kusan miliyan 200 a matsayin zama muhimmi wajen kyautata aikinsu.