1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Najeriya: Mabanbantan ra'ayi kan sojan haya

April 4, 2022

A yayin da a ke cigaba da neman mafitar rashin tsaro a sashen arewacin Najeriya, ra'ayi na banbanta tsakanin gwamnonin arewacin kasar da sauran jagororin yankin kan batun sojan haya da nufin kawo karshen matsalar

Yaki da 'yan ta'ada a Najeriya da Nijar
Hoto: Issouf Sanogo/AFP/Getty Images

Gwamnan jihar Kaduna Nasir El Rufain na zaman na baya bayan nan a cikin 'yan mulkin dake tunanin amfani da sojan haya wajen kawo karshen matsalar rashin tsaro a tarrayar Najeriya a wani abun dake nuna alamun dawowa daga rakiyar sojan kasar wajen iya kawo karshen matsalar tsaron.

Najeriyar dai ta kashe sama da Naira Triliyan hudu a cikin shekaru bakwai na masu tsintsiyar cikin neman mafita, amma kuma suna shirin karewa tare da kara ta'azzarar rikicin yankin arewa maso yammacin kasar.

Sai dai kuma kalaman na El Rufa'i na neman yamutsa hazo cikin kasar inda kungiyoyin farar hula da malaman addini ke cewa da sauran gyara a tunanin gwamnonin na arewa maso yamma.

Kungiyar ACF  ta dattawan arewacin kasar dai alai ga misali tace kuskure ne babba tunanin sojan haya da a cewar magatakardarta Mallam Murtala Aliyu suka gaza biyan bukata can baya.

Hoto: Jossy Ola/AP Photo/picture alliance

“An taba kawo irin wannan sojan haya a arewa maso gabas lokacin shugaba Jonatahn amma ba'a cimma irin nasarar da ake so ba. Ni ina ganin sojojinmu na da hazaka da kwazo da kwarewar magance wannan. Ina ga a basu dama su je su yi wannan yaki. Su yi fito na fito da 'yan ta'addan ba'a lallaba su ba”

Fito na fito da masu ta'adda ko kuma daukar sojan haya El Rufa'in dai na zaman gwamna na biyu cikin tsawon watani biyu da ya nemi taka rawar sojojin na haya. Ko a farkon watan Fabrairu dai dan uwansa na Borno Babagana Zulum yace sojan haya na iya sauya da dama a kokarin sake maido da zaman lafiya ga al'ummar ta arewa.

Ya zuwa yanzu dai sojan Wagner dake haya daga Rasha sun yi nasarar kwantar da hankula a kalla a kasashe Uku na Africa ta tsakiya da Mali da ma kasar Burkina Faso, ko bayan rawar da sojan Africa ta Kudu na Boer suka taka a kasashe daban daban a nahiyar. To sai dai a fadar Kabiru Adamu, duk da cewar hayar tana zaman salo a sassa daban daban na duniya, da kyar da gumin goshi suka kai ga haifar da nasara cikin tarrayar Najeriyar a halin yanzu.

Hoto: Getty Images/AFP/Stringer

“Akwai yarjejeniyoyi da yawa da muka shiga na kasa da kasa da suka hana mu amfani da sojan haya, na farko kenan, na biyu kuma irin tasirin da wadannan sojan ke yi a wasu kasashe ba dole bane su iya yi a Najeriya, saboda babu tsari na sa ido da kafa da za'a hau a cimma nasara kan harkar tsaro".

A takaice dai duk da sojan hayar na da tasiri a cikin yaki, akwai bukatar nau'i na sa ido ta yadda ba zasu ci zarafi ba. Koma dai yaya take shirin kayawa, batun tsaron na neman tasiri har ga siyasa da tattalin arzikin kasar. 

Akwai fargabar rashin tsraon da ya kai masu tsintsiyar bisa mulki, na iya kwace mulki a zaben shugaban kasar dake tafe. Kuma a fadar Farfesa Hafiz Abubakar dake zaman tsohon mataimakin gwamnan Kano masu tsintsiyar na da bukatar taka-tsantsan a cikin neman mafitar rikicin.

“Ai kowace gwamnati babban aikinta shine tabbatar da tsaro, wadannan abubuwa ba karamin kalubale bane. Amma dai mutanenmu sun san cewar wadanda suka bar wannan ba lallai suna da wani makami sama da APC ba.”

Abun jira a gani dai na zaman yadda take shirin kayawa a shekarar badi tsakanin APC dake kokawa cikin neman mafitar rikicin rashin tsaron da masu adawar dake kallon dama a cikinsa.


 

Tsallake zuwa bangare na gaba Bincika karin bayani