Najeriya: Mahara sun hallaka sojoji 12
December 16, 2018![Nigeria - Boko Haram Konflikt](https://static.dw.com/image/42684615_800.webp)
Talla
Kimanin sojoji 12 sun rasa ransu sakamakon artabu da 'yan Boko Haram masu dauke da makamai a yankin arewa maso gabashin Najeriya. Kamfanin dillancin labarai Reuters ya ruwaito wasu majiyoyi uku na sojoji na tabbatar da labarin, inda wasu sojojin da dama suka bace bayan gumurzun a jihar Borno. Sojojin sun ce soja daya ya rasa ransa lokacin da suka dakile wani hari daga 'yan na Boko Haram din cikin dare Jumma'a a wata karamar hukuma.