Najeriya: Majalisa ta amince da kasafin 2017
May 11, 2017Shugaban majalisar dattawan Najeriya Sanata Bukola Saraki shi ya jagoranci 'yan majalisar wajen amincewa da kasafin kudin na wannan shekara. Kasafin kudin da Shugaba Buhari ya mika wa majalisar a ranar 16 ga watan Disamba mai taken kasafin kudin farfadowa da bunkasa tattalin arzikin Najeriya, ‘yan majalisar sun tsara shi ne bisa sa ran samun hako mai ganga milyan 2.2, to sai dai ‘yan majalisar sun dora farashin na man fetir daga Dala 42.5 da shugaban Najeriyar ya gabatar zuwa Dala 44.5 a kan kowace gangar man fetir.
Sanata Barau Jibril na majalisar datawan Najeriya ya bayyana muhimman abubuwan da ke kunshe a kasafin kudin na wannan shekara, inda ya ce tsari ne da ba a taba yi ba.
A majalisar wakilan Najeriyar ma ‘yan majalisar sun amince da kasafin kudin bisa wannan adadi da ya nuna cewa duka majalisun biyu sun yi kari a kan abin da shugaban Najeriyar ya gabatar. A karon farko sashin gudanar da muhimman ayyuka ya samu kashi 30 cikin 100 wanda shi ne kaso mafi tsoka da aka baiwa sashin a 'yan shekarun nan, abi nda ya nuna sama da Naira tirliyan biyu aka kebewa sashin. Ko me suka hango suka yi wannan sauyi? Hon Sidi Yakubu Karasuwa ya ce a bana talaka zai dara.