1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Najeriya: Majalisa ta ba wa matasa ikon takara

Uwais Abubakar Idris
July 26, 2017

Majalisar datawan Najeriya ta jefa kuri’ar gyare-gyaren kundin tsarin mulkin kasar inda ta amince da 29 daga cikin sassa 33 da aka yi wa sauyi da suka kunshi ba wa kananan hukumomi 'yan cin gashin kansu.

Nigeria - Jugenddemonstration "not too young" in Abuja
Hoto: Uwais Abubakar Idris

Wadanda suka fi daukar hankali su ne amincewa ga dan takara mai zaman kansa ya shiga zabe a Najeriyar da kayadde wa'adin sau biyu ga shugaban kasa ko da kuwa ya gaji wanda ya rasu ne abinda ya kawar da yiwuwar dama sake takara ga tsohon shugaba Goodluck Jonathan.

Batun  baiwa kananan hukumomi 'yancin cin gashin kansu dai ya dauki hankali sosai. Sanata Kabiru Ibrahin Gaya wakili ne a kwamitin gyaran tsarin mulki ya bayyana abinda ya sanya su baiwa hukumomin 'yanci.

Ya ce "mun ba kanana hukumomi ‘yancinsu ba don komai ba saboda lokacin da na yi gwamna shekaru 24 da suka wuce kananan hukumomi su na cin gashin kansu. A lokacin ba'a ganin mutanen su na ta zuwa Abuja don su ce ‘yan majalisa su yi masu wani abu, kuma ba zaka ga yara na ta zaman kashe wando ba"

Hoto: picture-alliance/AP Photo/S. Alamba

Samun nasarar amince da rage shekaru ga masu shiga zabe da a yanzu wanda zai tsaya takara shugaban kasa da na dan majalisar datawan aka maida su shekru 35 daga 40 ya kasance abinda matasan Najeriyar ke murna da doki bayan matsin lamba da zanga-zangar da suka yi a kan batun. Ko me Sanata Abdul'Azeez Murtala Nyako zai ce wanda shi ne ya fara gabatar da kudurin?

Ya ce "dole ne mu yi  godiya ga Allah cewa wannan kudurin da na gabatar ya samu shiga domin a baiwa matasa damar su shiga harkar siyasa a dama da su sosai, kasan ita demokradiyya girma ta ke yi a hankali".

To sai dai akwai kudurorin da basu samu shiga ba kamar na  kirkiro da sabbin kananan hukumomi da batun baiwa mata kashi 35 na mukamai a kasar.

Hoto: Uwais Abubakar Idris

Matan da ke majalisar dai sun kaiga bara ga rashin nasarar basu kashi 35 na mukamai ya zama doka abinda Sanata Olujimi ta kaiga daga batun, shin me ya sanya su watsi da lamarin ne?

Abin jira a gani shi ne ko 'yan majalisar wakilai zasu bi sawu kafin kaiwa ga majalisun dokokin na jihohi da ka iya dakile duk wannan kokari  domin sai sun amince da sauye-sauyen kafin a kai wa shugaban Najeriya, abinda ya sanya bayyana cewa akwai sauran jan aiki a gaba.