Najeriya: Majalisa ta yi watsi da Magu
March 15, 2017Talla
Magu dai na zaman mai rikon mukamin shugaban hukumar ta EFCC. Wakilinmu na Abuja Abuja Uwais Abubakar idris ya ruwaito cewa majalisar dattijan ta ce ba za ta amince da shi ba, biyo bayan wani rahoto da ta ce ta samu daga hukumar tsaro ta farin kaya ta kasar wato SSS, wanda ya nunar da cewa ba shi da kimar da zai iya jagorantar hukumar ta EFCC, akwai cikakken rahoto a shirinmu na yamma.