Najeriya: Makiyaya sun samu makamai daga Libiya
April 13, 2018Shugaban Najeriya Mohammadu Buhari ya danganta yawan hare-haren da ake samu a wasu jihohin kasar da cewa, akwai hannun 'yan bindiga da tsohon shugaban Libiya Mu'ammar Gaddafi ya horar a shekarun baya, inda ya ce bayan mutuwarsa 'yan bindigar sun kutsa wasu kasashe da ke yammacin Afirka suna kai hare hare. Ko da yake wasu 'yan Najeriya basu gamsu da wannan hasashe na shugaba Buhari ba, to amma masharhanta irin su Shuaibu Zakari Lamba na gani kalaman shugaban su na kan hanya.
Duk da cewa gwamnatin Tarayyar Najeriyar tun a watanin baya ta umurci jihohin kasar da ke fuskantar wannan takkadama ta makiyaya da manoma, da su yi azamar kebe wuraren kiwon dabbobi domin samun masalaha, to amma jihohin sun yi watsi da umurnin, maimakon haka jihohi irin su Benue da Taraba, sun kafa dokar hana kiwo lamarin da ya kara janyo hare-haren 'yan bindiga. Yanzu dai al'ummar kasar sun zuba ido domin ganin lokacin samun saukin yawan hare-haren 'yan bindigar wanda wasu ke dangantawa da rikicin manoma da makiyaya.