1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ya dace Tinubu ya zabi Shettima mataimaki?

Uwais Abubakar Idris LMJ
July 11, 2022

Martani bayan da dan takarar neman shugaban kasa na jami'yyar APC mai mulki a Najeriya, Bola Ahmed Tinubu ya bayyana Sanata Kashim Shettima a matsayin matamakinsa.

Najeriya I Kashim Shettima I Tsohon Gwamnan jihar Borno
Tsohon gwamnan jihar Borno Kashim Shettima ne, zai yi wa Tinubu mataimaki a 2023Hoto: Reuters/A. Sotunde

Mtakin daukar Kashim Shettima a matsayin matamaki da Bola Ahmed Tinubu ya yi dai, ya nuna cewa dan takarar shugaban kasa da mataimakinsa dukkansu Musulmi ne, abin kuma da ya haifar da mayar da martani musamman daga Kiristocin Najeriyar da ke ganin ba a yi musu adalci ba kuma matakin ya sabawa tsarin mulkin Najeriyar.

Karin Bayani: Manyan jam'iyyun Najeriya na rasa 'ya'yansu

Bayyana suna shiyya da ma addini na mataimakin dan takarar neman shugabancin Najeriyar a jamiyyar APC mai mulki da aka yi dai, ya janyo kungiyar Kiristocin Najeriyar da take ganin kamanta adalci shi ne APC ta zabi mataimakin dan takarar Kirista. Kokari na raba siyasa da addini a Tarayyar Najeriyar dai ya ci tura, inda a wannan karon a fili shugabanin addinai ke nuna goyon bayansu ga dan takarar da ya kasance addininsu guda.

Dan takarar shugaban kasar Najeriya, na jam'iyar APC mai mulki Bola Ahmed TinubuHoto: Stefan Heunis/AFP/Getty Images

Baya ga batun marawa dan addini guda dai, akwai kuma kashedin batun dan wane bangare ne za a zaba ya tsaya takara. Sai dai wasu na ganin shigar da batun addini ko bangaranci a siyasar Najeriyar, ya yi watsi da batun cancanta ko kwarewa. Zafi da ma dacin da lamarin ya yi wa mutane da dama a Najeriya har da wadanda ma ba 'ya'yan jamiyyar APC ba ne, ya sanya dangata shi da cewa ya sabawa tsarin mulkin kasar.

Karin Bayani: Zaben fidda gwani ya bar baya da kura 

Duk da cewa dan takarar neman shugabancin Najeriyar a karakashin APC Bola Ahmed Tinubu dai, ya bayyana dalilan jam'iyyarsa na zaben Musulmi daga shiyyar Arewa maso Gabashin Najeriyar a matsayin mataimakinsa da alamu wannan batu zai zama wanda za a yi yakin neman zabe da shi, a zaben da ake ganin zai fi kowane dau kar hankali a Najeriyar tun bayan sake kafa dimukuradiyya a kasar.

 

Tsallake zuwa bangare na gaba Bincika karin bayani