Martani kan batun kare kai daga 'yan bindiga
February 18, 2021Ana dai cigaba da neman hanyoyin neman kai karshen annobar rashin tsaron da tai aure tana shirin tarewa a cikinl tarrayar Najeriya. Suma gwamnoni na kasar sun share wunin wannan Alhamis suna nazarin hanyoyin tunkarar matsalar ta tsaro, an kamalla taron gwamnonn tare da yanke hukuncin haramta kiwo irin na gadon gado.Nadin sababbin hafoshin tsaro a Najeriya
Gwamnonin sun kuma ce daga yanzu za'a biya diyya ga duk wanda aka yi wa ta'adi daga rigingumun rashin tsaron kuma wadanda suka rasa ransu za su sami Jana"izar da ta dace.To sai dai kuma wasu kalaman ministan tsaron kasar, Janar Bashir Magashi dai na ci gaba da daukar hankula a tsakanin al'umma ta kasar bayan da Janar Magashin, ya nemi 'yan kasar da su kare kansu saga maharan da ya ce makamansu ba su taka kara sun karya ba.Buhari: Ba wadatar kudin yakar ta'addanci
Kalaman kuma da a cewar kaftin Abdullahi Bakoji da ke sharhi cikin harkar ta tsaro na iya sanyaya zuciyar al'umma ta kasar da ke fatan samun kariya ta 'yan mulki na kasar. Jami'an tsaron kasar dai sun ce suna karin azama da nufin ceto 'yan makarantar Kagara. Kuma rundunar yan sanda ta kasar tace ta tura jiragen shawagi da karin yan sanda na musamman yankin da nufin kara karfafa bincike a dazukan yankin, ko bayan nan dai gwamnonin sun kuma ce za'a kara inganta tsaro a kan iyakokin tarrayar Najeriya.