Najeriya: Martani kan kisan Fulani makiyaya
January 26, 2023Baya ga Fulani makiyaya akwai Hausawa mahauta da harin ya rutsa da su yayin da wasu da dama suka jikkata. Barrister Bello Danbaba na cikin mutanen da abin ya faru a gaban idanunsu wanda yace akwai kaninsa cikin wadanda aka kashe.
Tun bayan bullo da dokar hana kiwo a fili da gwamnatin jihar Benue ta yi ake fama da rigingimu tsakanin makiyaya da manoma a jihar. Tuni kungiyar Miyetti Allah ta Fulani makiyaya ta mayar da martani inda ta yi Allah wadai da harin tare da neman a yi wa wadanda aka kashe adalci.
Gwamnatin jihar Nasarawa ta nemi da a kwantar da hankali kan cewa za ta dauki matyakin da ya dace domin ana bincike a kan lamarin.
Koda a shekarar 2022 sai da aka samu kai hari ta jirgin sama a kan makiyaya a jihar Nasarawa, abin da ke nuna yanayin rashin tsaron da ake fuskanta. Fulani makiyaya da manoma dai sun dade suna zaman lafiya a tsakaninsu a shekarun da suka gabata, yanayin da ake fatan dawo da shi.