1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
Lafiya

Najeriya: Masu Corona sun haura dubu daya

Ahmed Salisu
April 25, 2020

Yawan wadanda ke dauke da cutar Coronavirus a Najeriya na cigaba da karuwa, inda a jiya Juma'a hukumar da ke yaki da cutuka masu yaduwa a kasar wato NCDC ta ce an samu karin mutum 114 da aka tabbatar sun kamu da cutar.

Symbolbild Corona-Virus
Hoto: Reuters/D. Ruvic

Jihar Legas da ke kudancin kasar ce kan gaba a yawan sabbin kamun yayin da jihar Zamfara da ke arewaci ke zaman jiha ta baya-bayan nan da da cutar ta bula, inda aka samu mutum biyu da suka harbu. Gwaman jihar ta Zamfara Bello Matawalle ya bayyana kaduwarsa bayan samun labarin bayyanar cutar, inda ya shawarci al'ummar jihar kan su dau matakan kariya.

Wadannan sabbin alkaluman da NCDC din ta fidda sun kawo yawan wanda suka kamu da cutar ta Covid-19 din zuwa 1095 inda 208 daga cikinsu suka warke sai kuma mutum 32 da yanzu haka aka tabbatar sun rasu.