1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Matakan rigakafin cutar Corona a Najeriya

Uwais Abubakar Idris GAT
January 29, 2020

Gwamnatin Najeriya ta bayyana daukar karin matakai na rigakafin hana bayyanar cutar Coronavirus a kasar, tare kuma da yin kira ga jama’a da su kwantar da hankalinsu a kan wannan lamari. 

Symbolbild Forschungsbeziehungen Deutschland Afrika
Hoto: picture-alliance/Ton Koene


Kokari na kwantar da hankalin al'ummar Najeriya a kan wannan cuta da ya sanya daukar matakai da ma kafa kwamiti na musamman da ya hada da jami’an kula da kare lafiyar al'umma da jami’an tsaro da kuma na sufurin jiragen sama, inda gwamnatin ta ce jami’anta na sa ido tare da gwada mutanen da ke shigar kasar domin karesu. Ministan kula da lafiya na Najeriyar Osagie Ehanire ya zayyana matakan da ake dauka a kasar:


"Yanzu haka sashin kula da lafiya a tashoshin shigar Najeriya na aiwatar da matakan dakile shigar cutar Coronavirus zuwa kasar, don haka ma’aikatar lafiya na bai wa al'umma tabbacin karfin da take da shi na ganowa, bincikawa da kuma dakile wannan matsala. Baya ga wannan cibiyar kula da kare cututtuka ta samar da cibiyar kula da cutar Corona, kuma a shirye take da zaran samu bullar cutar a Najeriya’’. 

Hoto: DW

 
Daukar matakai a kan iyakokin Najeriya ya zama muhimmin mataki da ba kawai ke kwantar da hankalin al'umma ba, yake ma sanya karin bayani na cewa cutar Coronan fa ba wacce ya kamata ta razana al’umma ba ce, domin akwai cututtukan da suka fita illa, kuma bisa matakn da ake dauka babu abin daga hankali a kai. 


Al'umma dai na cike da fata bisa ga matakan da gwamnatin ke dauka da ma bukatar karin bayanai na hanyoyin samun kariya da al’umma za su bi musamman zuwa asibiti da zarar sun ji ba dai dai ba. Domin hukumar kula da kare ‘yancin masu sayen kaya ta Najeriyar ta rufe wata kasuwa a birnin Abuja, wacce  ake zargin an shigo da kayan abincin dangin kifi ta haramtaciyyar hanya, kayan da ake bincike a kansa.

Hoto: CARL DE SOUZA/AFP/Getty Images