1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Najeriya: Matakan yaki da fataucin Jama'a

Uwais Abubakar Idris
January 9, 2024

Najeriya ta bullo da sabbin hanyoyin yaki da masu fataucin jama'a da kuma kaura ta haramtacciyar hanaya zuwa Turai

Kwarar 'yan gudun hijira zuwa Turai
Kwarar 'yan gudun hijira zuwa TuraiHoto: Ferhi Belaid/AFP/Getty Images

Bullo da sabbin dubaru a dai dai wannan lokaci da ake fsukantar kalubale daban daban muhimmin mataki ne a kokarin shawo kan matsalar. Hukumar da ke yaki da fasa kwaurin bil Adama ta Najeriyar ta bayyana cewa akwai bukatar fahimtar cewa babu wanda ya hana kaura ta hanyar da ta dace bisa samun takardu da izini. Hukumar ta yi kashedin kauce wa yaudara da hatsarin da ke fuskntar masu wannan mummunan hali. 

Abin da yafi daga hankali shine mumunan halin da wadanda suka tsinci kansu a cikin matasalar fasakwaurin bani Adama kan shiga. 

Karin Bayani: Karuwar masu kaura tsakanin kasa da kasa

Najeriyar dai na cikin kasashen da ke nuna damuwa a kan sabon matakin da gwamnatin mulkin sojan jamhuriyar Nijar ta dauka na dage laifin fataucin jama'a a matsayin babban laifi a kasar, abinda MS Dogara ya bayyana a matsayin babban kalubale da ke fuskantar Najeriya.

Ana fatan bullo da sabbin dubaru na amfani da rubutun zube, wasan kwaikwayo da tsananta hukunta masu laifin zai taimaka rage kaifin wannan matsala wacce duk da matakan da ake dauka ake samun masatan da ke kutsa kai a cikinta.