Najeriya: Matsalar kiwon shanu a Abuja
September 12, 2025
Shugabanin makiyaya watau ardo ardo a karkashin kungiyar Miyetti Allah da jami'an gwamnatin Najeriya suna kokarin lalaubo mafita daga matsalar baza shannu a kan tituna a Abuja babban birnin tarayyar Najeriya.
Sun yi kokarin jiffar tsuntusu biyu da duste daya domin tsara dabarar ilmantar da yayan makiyaya domin rage yawan yaran da basa zuwa makaranta.
Karin Bayani:Rikicin Fulani da Makomar kiwo a Najeriya
Mai alfarma sarkin Musulmi Sultan Sa'ad Abubakar na uku wanda ya jagoranci taron da aka yi da wakilan makiyaya a Abuja, ya bayyana muhimmancin matakan da aka dauka domin shawo kan matsalar a matsayin hanyar samun ci gaban kasa..
Karin Bayani:Martanin Fulani ga shawarar gwamnatin Kano
An kafa kwamiti da zai tattara dukkanin korafe-korafe da ardo-ardo suka yi da suka hada da rashin tsaro, cin zarafi daga jami'an tsaro da sauran matsaloli da suke fuskanta.