1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Matsalar tsaro ta yawaita a Najeriya

Lateefa Mustapha Ja'afar
July 23, 2020

Al'ummar yankin Arewa maso Yamma da kuma Arewa maso Gabas a Najeriya na cikin halin tasku, sakamakon matsalar rashain tsaro da ake fama da ita.

Karrikatur  Nigeria Sicherheit

Tsawon shekaru ake fama da matsalar Boko Haram a Najeriya musamman yankin Arewa maso Gabas, kwatsam sai matsalar 'yan bindiga ta bullo a jihohin yankin Arewa maso Yamma. A yanzu dai kusan kullum sai an samu hare-hare ko dai na 'yan bindiga ko kuma na Boko Haram.

Ko da a baya-byan nan ma sai 'yan bindigar suka halaka mutane ciki har da jami'an tsaro a Katsina, yayin da a karon farko aka samu fashewar bom a jihar. A jihar Borno ma dai labarin guda ne, inda mayakan Boko Haram musamman bangaren da suka ce suna da alaka da kungiyar 'yan ta'addan IS, suke ci gaba da halaka mutane da suka hadar da fararen hula da  jami'an tsaro da ma'aikatan agaji.

Tsallake zuwa bangare na gaba Rahotanni da Sharhuna