1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Matsaloli na kara yawaita a Najeriya

Lateefa Mustapha Ja'afar
March 17, 2022

A daidai lokacin da ya rage kasa da shekara guda a gudanar da babban zabe a Tarayyar Najeriya, matsalolin tattalin arziki da rashin tsaro da ma rikicin siyasa na kara kamari.

Zanen Barkwanci I Najeriya I Matsaloli
Zanen barkwanci kan halin da Najeriya ke ciki

Matsalolin da Najeriyar ke fuskanta dai, sun hadar da batun matsalar tsaro, musamman farmakin da 'yan bindiga ke kai wa a jihohin yankin Arewa maso Yamma da kuma tsakiyar kasar. A yanzu kuma kasar na fuskantar matsaloli a siyasance, musamman ma rikicin cikin gida da ya mamaye manyan jam'iyyun kasar ciki kuwa har da APC mai mulki. Ita ma dai babbar jam'iyyar adawa ta PDP, na fama da kalar nata rikicin.

Matsalar baya-bayan nan dai, ita ce ta karancin man fetur da ta haifar da rashin hasken wutar lantarki da ma ruwan sha. Baya ga haka malaman jami'o'in kasar sun tsunduma yajin aikin gargadi da uska kara wa'adinsa daga makonni hudu zuwa takwas. Kara wa'adin yajin aikin gargadin na malaman jami'o'in kasar dai, na zuwa ne a daidai lokacin da shugabn kasar Muhammadu Buhari ya tafi birnin London na kasar Birtaniya domin ganin likita.

Tsallake zuwa bangare na gaba Rahotanni da Sharhuna