Mene ne aikin dan sandan Najeriya?
November 11, 2025
Kiyasi ya nunar da cewa a Najeriyar da ke da 'yan sanda kasa da 400,000, dan sanda daya na gadin mutanen da yawansu ya kai 600. Wannan dai, na kara fito da annobar rashin tsaron da kasar ke fama da shi. Ya zuwa yanzun dai 'yan sandan sun bace a kauyuka da daman gaske, yayin da hankali ya koma ga birane.
Karancin 'yan sanda a ksa mai yawan jama'a
Abun kuma da ke kara ta'azzarare kisa da ma zubar jini, inda wani rahoto wata kungiyar Tarayyar Turai da ke kula da harkar mafaka ya ce a cikin 'yan sanda kasa da 400,000 da ake da su a kasar, kaso 25 na tafiya ne zuwa ga ofisoshi da gidajen manya yayin da ragowar ke da jan aikin kare 'yan kasar miliyan 230. Batun rashin yawa da kayan aikin 'yan sandan dai, na zaman daya cikin na kan gaba a dalilan rashin tsaron da Najeriyar ke fuskanta.
To sai dai kuma ko ya zuwa ina rundunar 'yan sandan ke iya kai wa a tsakanin neman kudin shigar rage nauyi da kuma bayar da kariya cikin yanayi maras kyau, matsalar rashin kudi da kayan aikin ko bayan rashin isassun masu kayan sarkin na taka rawa wajen ta'azzarar rashin tsaron da ke ta yaduwa cikin kasar.
Babu kayan aiki da albashi mai kyau
Ko a bana dai ga misali majalisun kasar sun rage kasafin kudin 'yan sandan, ragin kusan kaso 30 cikin 100. Isa Sunusi dai na zaman shugaban kungiyar Kare Hakkin dan Adam ta Kasa da Kasa Amnesty International, kuma ya ce ana bukatar janye 'yan sandan daga cikin gidajen manya da nufin inganta tsaro a tituna da ma cikin gidajen talakawa.
A cikin tsakiyar shekarar bana dai, faifen bidiyon wani dan kasar Chaina yana cin zarafin wani jami'in dan sanda ya tayar da hankali a Tarayyar Najeriyar. Ya zuwa yanzun dai, 'yan sandan na neman su bace daga kauyuka da karkarar Najeriyar da nufin kare biranen da ke komawa tungar rikicin rashin tsaro.