Mota ta hallaka yara 11 a jihar Gombe
December 21, 2016Talla
Hadarin ya faru ne a dai dai lokacin da ake karatun Mauladin tunawa da ranar haihuwar Monzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, a cewar hukumar 'yan sandan jihar. Katsewar birkin motar ne dai ya haddasa wannan hadari a cewar Ahmed Usman, daya daga cikin masu magana da yawun 'yan sandan, inda ya ce yaran sun kasance 'yan shekaru 11 zuwa 15 da haihuwa.
Wannan hadari dai ya harzuka jama'ar da ke wurin, inda nan take suka hau direban motar da duka, har sai da ya mutu. A kowace shekara dai, Musulmi a arewacin Najeriya, da ma duniya, na bikin tunawa da ranar haihuwar Annabi Muhammed yardar Allah ta tabbata a gare shi na tsawon makonni, inda ake samun halartar dumbun jama'a.