1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Tankiya kan daukar sojojin haya a Najeriya

December 3, 2020

 A ci gaba da kokarin neman mafitar rikicin rashin tsaron da ke neman wucewa da sanin 'yan mulkin tarrayar Najeriya, muhawara ta barke cikin kasar bayan shawarar gwamnan Borno ta sake komawa ya zuwa soja na haya.

Nigeria Boko Haram
Hoto: Lekan Oyekanmi/AP Photo/picture alliance

Duk da cewar dai cika burin zabe ya saka tsohuwar gwamnatin tarrayar Najeriyar gwada sojan na haya a kan hanyar neman karshen aiyyuka na Boko ta Haram , gwamnatin ba ta ji cikin dadi ba sakamakon adawa da shirin da 'yan kasar suka rika yi wa kallon kokari na zagon kasa ga jami'an tsaron tarrayar Najeriya. To sai dai kuma shekaru biyar can baya daga dukkan alamu batun na sake shigar sojojin na haya ya fara daukar hankali na 'yan kasar bayan kisan manoman Zabarmari da ke a Jihar Borno. Gwamnan Jihar ta Borno Babagana Zulum dai ya ambato sojan na haya da ya ce su dauki alhakin shiga dajin Sambisan a matsayin daya a cikin jeri na shawari guda shida da Bornon ke kallon na iya kare tada hankalin al'ummar yankin. Shekaru biyar can baya dai tsohon shugaban kasar Goodluck Ebele Jonathan ya shigo da sojojin na haya 250 daga Afirka ta Kudu da suka taka rawa a cikin yakin na ta'addanci a wani abin da ya dauki hankali na 'yan kasar da ke masa kallon kokari na tabbatar da gazawa ta jami'an tsaron Najeriyar da ke jagorantar yakin.

Gazawar sojojin Najeriya a kallamun da gwamnan Borno ya ambato

Farfesa Babagana Umara Zulun gwamnan Jihar BornoHoto: Government House, Maiduguri, Borno State

To sai dai kuma matsayin na Zulum din da tun da farkon fari ya nuna rashi na gamsuwa bisa rawar sojoji a cikin yakin dai tuni ya fara nazari a cikin kasar da ke kallon rawa ta sojan na haya da idanu dabam-dabam. Dr Umar Ardo dai na zaman masani a kan tarihin soja, da kuma ya ce sojojin na haya ba su da tarihi na biya ta bukata walau a Mozambik ko kuma yankin yammaci na Sahara da ke cikin tada hankali da Moroko. Tarrayar Najeriyar dai ta rika biyan darurruwan miliyoyi na daloli ga kamfanin kasar ta Afirka ta Kudu da sunan taimaka mata kai karshen annobar ta Boko ta Haram har ya zuwa hatsarin da ya kai ga asarar ran daya a cikin sojan na haya da ya tona asiri na gwamnatin da ta dauki lokaci tana boye shi.

Rashin kudi da kayan aiki ya janyo cikas wajen kula da lamarin tsaro a Najeriya

Hoto: Getty Images/AFP/I. Sanogo

Sake hayar sojan dai na tabbatar da gazawar sojoji na kasar da suka share shekara da shekaru amma kuma suka gaza samun nasara a kan kungiyar ta Boko Haram. To sai dai kuma a fadar Captain Abdullahi Bakoji da ke sharhi kan harkar tsaron kasar dai kisan kudin wajen kayan aiki na zaman mafita ga kasar maimakon dauko sojan da ke bautawa kudi. Rashin kudi da kayan aiki dai na zaman na kan gaba cikin dalilan gazawar sojan , ko bayan sanyin gwiwa a bangare na 'yan kasar da a kusan kullum ke kokarin dawo daga rakiyar jami'an tsaron. Najeriyar ta share sama da shekaru 11 tana kallon rikidar yakin daga fito na fito da masu dinkin hula ya zuwa tunkarar yan ta'addar da ke zaman na kan gaba ga batun hatsari a duniya baki daya.