Muhawarar neman sake fasalin Najeriya ta kara zafi
September 5, 2018Duk da cewar har ya zuwa yanzu an gaza samun daidaito a bisa ma'anar sauyin fasali a cikin Tarrayar Najeriya, sannu a hankali muhawara a tsakani na kwararru da ma masu takama da siyasa ta kasar na kara karuwa a bisa neman sake fasali ga kasar.
Wasu dai na kallon batun sake fasalin hanyar rabo ga tattali na arzikin kasar, wasu kuma na kallon tsari na jihohi da kananan hukumomi da ma ayyukan da suke yi, a yayin kuma da wasu ke neman cin gashin kansu duk dai a cikin inuwar sauyin.
Tun bayan 'yancin kan kasar shekaru kusan 60 baya dai jijiyar wuya ke tashi daga bangarori na kasar da ke ganin an masu ba dadi a cikin fasalin da ke da sunan Tarrayar Najeriyar.
Ana dai kallon gaza ci-gaban kasar zuwa babban matsayi dai na da ruwa da tsaki da tsarin da take dauka, tsarin kuma da ya ba da karfi sosai a cikin mulkin tsakiya tare da mayar da bangarori masu biyayya ko sun ki, tsarin kuma da a cewar Dr Kole Shettima da ke zaman shugaban cibiyar inganta dimukuradiyya da ci-gaba da ke a Abuja yake bukatar sauyin fasali a bisa neman daukar kasar zuwa tudun mun tsira.
Kokari na dauki karfi daga tsakiya ko kuma kokari na ginin sababbin mammalaka al'umma dai, an dauki lokaci ana ta korafi sakamakon mika kananan hukumomi na kasar ya zuwa ga jihohi.
To sai dai kuma a fadar Isa Tafida Mafindi dan siyasa kuma mahalarcin taruka dabam-dabam bisa makoma ta kasar, biyan bukatar talaka na zaman na kan gaba maimakon gina sababbin allolli a jihohi a cikin sunan sauyi.
Ba dai sabon batu ba ne sauyin tsarin da kasar ke tafiya kai, to sai dai kuma daga dukkan alamu kokari na biya na bukata a bangare na sassa na kasar dai ya sa muhawarar daukar zafi da kila ma launi na siyasa.
Kuma a fadar shi kansa ministan shari'ar Tarrayar Najeriya, Abubakar Malami, gwamnatin kasar na kallon sabuwar muhawarar da idanu na guguwar siyasar da take kadawa cikin kasar a halin yanzu.