1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Martani bayan soke SARS a Najeriya

October 12, 2020

Kasa 'yan sa'o'i da rusa rundanar 'yan sanda ta SARS a Najeriya da ke yaki da masu manyan laifuka, matasan kasar da suka share lokaci suna matsa lambar kai karshen rundunar na tsallen murna.

Nigeria Lagos | Protest EndSARS
Zanga-zangar matasa da kungiyoyi ta tilasta rusa rundunar SARS a NajeriyaHoto: Adekunle Ajayi/NurPhoto/picture-alliance

Kama daga 'ya'yan sarakuna zuwa talakawa na kasar dai, matasan sun kau da jerin banbamcin girma na iyaye da kila ma  addini da kabila, wajen fitowa domin nuna adawa da rawar da 'yan sandan na SARS ke takawa da nufin cin zarafi na 'yan kasar. Kungiyoyi dabam-dabam cikin kasar da ma gungu na matasa dai, sun share tsawon daukacin makon jiya suna zanga- zangar neman kai karshen ayyukan rundanar SARS din da ake zargi da wuce gona da iri wajen cin zarafi na matasan Najeriyar, kafin sanarwar babban sufeton 'yan sanda na kasar Mohammed Adamu kan matakin rusa rundanar tare da baza 'ya'yanta cikin ragowar 'yan sandan.

Karin Bayani:  Gyara ga tsarin 'yan sandan Najeriya

Isa Sunusi dai na zaman kakaki na kungiyar Amnesty International mai fafutukar kare hakkin dan Adam a Tarayyar Najeriyar da ya ce matakin na hukumomin 'yan sandan na zaman sabon babi a cikin harkar mulki ta kasar.
Koma ya zuwa ina hukumar 'yan sandan suke shiri su kai da nufin cika buri na matasan Najeriyar, a fada a cika dai na zaman tunanin matasan da ke fadin sun sha sauraro na kalamai dadada, ba tare da cika alkawarin jami'an tsaron kasar ba. To sai dai kuma in har 'yan mulki na kasar suna shirin sauraro na bukatu na matasan dai, daga dukkan alamu suna shirin ji da yawa ko bayan cin zarafi a banagren 'yan sandan.

Sfeto janar na 'yan sandan Najeriya ya sanar da rusa rundunar SARS

Karin Bayani: Kwaskwarima ga aikin rundunar SARS a Najeriya

Kuma ko bayan batun zama na lafiya dai, a fadar Bello Shagari da ke zaman tsohon shugaban kungiyar matasan Nnajeriyar, matasan kasar suna shirin kai wa har ya zuwa batun mulkin kasar da suke fadi ana ci da guminsu. Shagarin dai na ya ce 'yan sandan na SARS sun taka sun kuma kai wa ga zubarwa a cikin ayyukan kare 'yan kasar daga annoba ta fashi da makami da ragowar damfarar da ake zargi na matasan kasar aikatawa.

 

Tsallake zuwa bangare na gaba Bincika karin bayani