Yan bindiga sun kai hari jihar Imo
April 22, 2023Rahotanni daga Najeriya sun sheda cewa, wasu 'yan bindiga da ba a kai ga gano ko su wane ne ba, sun hallaka jami'an 'yan sanda biyar da wasu fararen hula biyu a yayin wani hari da suka kai a jihar Imo da ke kudu maso gabashin kasar, Mista Henry Okoye, wanda shi ne kakakin rundunar 'yan sandan jihar da ya tabbatar da labarin ya ce, an kai harin ne a ranar Jumma'ar da ta gabata amma ba tare da ya yi wani karin bayani ba.
Jihar Imo kamar sauran jihohin da ke kudu maso gabashin Najeriyar na fama da hare-haren 'yan bindiga da ke lakume rayuka da ma barazana ga zaman lafiya. A baya jami'an tsaron yankin na zargi da ma danganta ire-iren wadannan hare-haren da sa hannun Kungiyar IPOB ta 'yan rajin kafa kasar Biafra, sai dai IPOB din ta sha musanta zargin.