Najeriya na bikin samun 'yanci
October 1, 2022Talla
A Asabar din ne Najeriyar ke cika shekaru 62 da samun 'yanci daga turawan mulkin mallaka na Birtaniya, bikin da ke zuwa daidai lokacin da al'amuran siyasa ke daukar harami.
A jawabin da ya gabatar wa 'yan kasar, Shugaba Buhari ya yaba kokarin da gwamnatinsa ta yi cikin wa'adinta biyu na mulki, duk kuwa da cewa ya lura da wasu matsalolin da kasar ke fama da su.
'Yan Najeriyar dai na bayyana ra'ayoyi mabambaata game da ranar ta 'yanci, musamman ganin yadda kasar ke fama da tarin matsaloli a fannin tattalin arziki da kuma na tsaro.