1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Najeriya na shirin fara kwaso 'yan kasarta daga Sudan

April 24, 2023

A yayin da ake ci gaba da zaman dar-dar a tsakanin dubban 'yan Najeriya da ke kasar Sudan, gwamnatin tarrayar Najeriya ta ce ta na shirin fara aikin kwaso dubban 'yan kasar daga wannan Litinin

Hoto: The Yomiuri Shimbun/AP/picture alliance

Dalibai tsakanin 5,500 zuwa 13,000 ne ake jin sun makale a yakin da ke faruwa a Sudan ya zuwa yanzu. Abun kuma da ya tada hankali a tarrayar Najeriya in da dubban iyaye da ma ragowar dangi ke ta korafin ta yi baki ta na shirin lalacewa yanzu.

Mako sama da guda da barkewar yakin dai har yanzu babu ko dan Najeriyar guda daya da ya iso cikin kasar a wani abun da ake yiwa kallo na gazawa a bangaren masu mulkin kasar.

To sai dai kuma Abujar ta ce ta samo izinin sojan kasar ta Sudan kuma ta na shirin fara kwashe daliban a wannan Litinin din a cewar kakakin fadar gwamnatin kasar malam Garba Shehu.

Tuni dai kamfanin jirgin sama mafi girma a cikin tarrayar Najeriyar na Air Peace ya bayyana aniyarsa ta shiga cikin shirin kwashe daliban da ke tsakiyar rikicin.

Abujar ta ce ta tanadi motocin sufuri don tabbatar da kwashe daliban da ma ragowar jami'ai na ofishi na jakadancin Najeriya da su kansu ke cikin kasar Sudan din a halin yanzu

To sai dai kuma a fadar Zainab Shaibu daya daga cikin iyayen da 'ya'yansu ke makale a can a birnin Khartoum ta ce suna iya magana dasu daga lokaci zuwa ga lokaci.

Akwai dai korafi na karancin abinci ko bayan barazanar rayuwa ga daliban daga rikicin da ya kai ga killace su cikin gidaje da nufin kauce wa rikicin.