1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Najeriya na shirin kwaso 'yan kasarta daga Afirka ta Kudu

May 4, 2026

Hukumomin Najeriya sun sanar da shirin dawo da 'yan kasar da ke zaune a Afirka ta Kudu zuwa gida, biyo bayan hare-haren kiyayya kan baki da aka rinka kai musu a makonnin da suka gabata.

Ecowas-Treffen in Nigeria | Bola Tinubu
Hoto: Gbemiga Olamikan/AP/dpa/picture alliance

Ministar harkokin wajen Najeriya, Bianca Odumegwu-Ojukwu ta sanar shirin duba yiwuwar dawo da 'yan kasar da ke da ra'ayin koma wa gid adaga Afirka ta Kudu sakamakon karuwar hare-hare da ake kai wa baki. Jami'ar diflomasiyyar ta ce tuni aka samu 'yan Najeriya kusan 130 da suka bayyana aniyar komawa gida, kuma ana sa ran adadin zai iya karuwa nan gaba.

Najeriya ta gayyaci jakadan Afirka ta Kudu

Madam Odumegwu-Ojukwu ta kuma jaddada cewa ba za a taba lamunta ba rayuka da dukuyoyin 'yan Najeriya da ke zaune a Afirka ta Kudu su ci gaba da kasancewa cikin hadari.

Bugu da kari ministar ta kara da cewa akalla 'yan Najeriya biyu ne suka mutu sakamakon lamarin na baya-bayan na, inda ta yi zargin cewa wadannan halaye na nuna kiyayya ga baki sun sake tasowa ne gabanin zaben Afirka ta Kudu, inda jam'iyyun adawa masu kyamar baki ke amfani da yanayin domin samun kuru'in jama'a musamman matasa marasa aikin yi.

Tsallake zuwa bangare na gaba Babban labarin DW

Babban labarin DW

Tsallake zuwa bangare na gaba Karin labarai daga DW