Cece-kucen kisan fararen hula a Najeriya
December 22, 2022Duk da cewar dai an yi nasarar halaka da dama a cikin masu takama da fashin daji, kan harbin kan mai uwa da wabin da aka yi a wasu kauyuka guda biyu a karamar hukumar Dan Sadau da ke jihar Zamfara na ci gaba da jawo kace-nace da ma nuna damuwa kan tsarin ayyukan sojoji na saman Najeriyar. Akalla fararen hula 45 ne harin na farkon mako ya halaka baya ga sama da 20 da suka jikkata, a bin da ya tayar da hankali kuma ke janyo damuwa. To sai dai kuma a wani abu da ke zaman sabo fil, Abujar ta bakin ministan yada labarai kana kakakin gwamnati Alhaji Lai Mohammed ta yi ban hakuri ga harin da ta ce tana bakin ciki da afkuwarsa.
Sabon harin da yai sanadiyyar kisan fararen hula mafi yawa a cikin yakin na Zamfara dai, tuni ya fara janyo kiran bukatar bincike da nufin tantace aya cikin tsakuwar ainihin abin da ya faru. Na baya-baya dai na zaman kungiyar kare hakkin dan Adam ta kasa da kasa Amnesty International da ta nemi bincike da yin hukunci kan laifin da a fadar Auwal Musa Rafsanjani da ke zaman shugabanta a Najeriya, ban hakurin gwamnatin bai isa ba. Koma wane mataki gwamnatin Najeriyar take shirin da ta dauka gaza bambance tsakanin fararen hular da 'yan ta'addar dai, na kara jawo damuwa har a tsakanin kwarraru da ke fadin akwai rashin tsarin aiki. Akwai dai tsoron ci gaba a cikin harin, ka iya kai wa ya zuwa rusa dangantaka tsakanin jami'an tsaron da ragowar jama'ar garuruwan da ke neman mafitar rikicin.