1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Nnamdi Kanu a hannun jami'an DSS

June 29, 2021

A wani abun da ke zaman gagarumi na ci gaba a kokarin sake mayar da fatalwar Biafra, gwamnatin Tarayyar Najeriya ta sake gurfanar da shugaban gwagwarmaya da awaren Biafran Nnamdi Kanu a gaban kuliya a Abuja.

Nigeria Biafra | Nnamdi Kanu
Nnamdi Kanu ya shiga hannun mahukuntan NajeriyaHoto: DW/K. Gänsler

Wannan ne dai karo na biyu cikin shekaru shida da gwamnatin Najeriyar ke gabatar da jagoran na awaren Biafran Nnmadi Kanu da take zargi da ayyuka na ta'addanci. Babu zato ba kuma tsamani mahukuntan Tarayyar Najeriyar suka sanar da sake kame jagoran na IPOB da ya tsere zuwa Ingila, ya kuma rika tunzura kokarin awaren daga can. Wata sanarwar ministan shari'ar kasar Abubakar Malami dai, ta ce kungiyar 'Yan Sandan Kasa da Kasa Interpol da jami'an tsaron Najeriyar ne suka  jagoranci aikin sake kame madugun awaren, ta kuma mika shi hannu na jami'an tsaron kasar a karshen makon da ya gabata.

Karin Bayani: IPOB na shirin zaman dirshan a Najeriya

Tuni dai  Abujar ta sake mayar da Kanun zuwa kotu, domin ci gaba da fuskantar jerin tuhumomi har 11 da yake yi kafin tserewar tasa. Kotun  kuma da a karkashin mai shari'a Binta Nyako ta bayar da umarnin ci gaba da tsare shi a hannun jami'ain tsaron Najeriyar na farin kaya DSS har ya zuwa 27 ga watan Yuli mai zuwa. To sai dai kuma kamen nasa ya dauki hankali cikin kasar, a tsakanin kwararru da ma lauyoyin da ke ba shi fassara iri-iri. Kabiru Adamu dai na zaman mai sharhi a kan tsaron da kuma ya ce duk da ta'annatin Nnmadi Kanun daga Ingila, akwai bukatar taka tsan-tsan a bangaren mahukuntan kasar da nufin kauce wa zargin nunin fififko a cikin yakin sake kwantar da hankula a kasar.

Masu rajin kafa kasar Biafra a Najeriya, na nan a kan bakansuHoto: Getty Images/AFP/P. U. Ekpei

Koma ya take shirin kayawa a tsakanin daruruwan magoya bayan Kanu da hukumomi na gwamnatin Najeriyar dai, rahotanni daga Owerri fadar gwamnatin jihar Imo da ke yankin na Kudu maso Gabas din, na nuna tsallen murna daga bangaren matasan yankin na Kudu maso Gabas da ke ji ba dadi, sakamakon gwagwarmayar da ta rikide ya zuwa zubar jini da asara ta dukiya ba adadi a cikin yankin. To sai dai kuma Kanun da ke da alamun rama, ya shaidawa kotun ta Abujar cewar barazana ga rayuwarsa ce ta sa shi tserewa ya bar kasar bayan belin da ya samu.

Karin Bayani: Kama masu rajin kafa kasar Biafra a Najeriya

Da kamar wuya dai a tunanin Barrister Buhari Yusuf da ke zaman wani lauya mai zaman kansa cikin kasar, Kanun ya same ta da sauki a cikin kotun da ke da babban aikin yanke hukunci kan makomarsa tsakanin jagora na awaren Biafra da kuma dan kurkukun da ke iya share shekaru a hannun makiya. Sake kamen Kanun dai daga dukkan alamu, na iya aika babban sako a ciki da ma wajen Najeriyar ga masu ja da hukuma walau a yankin Arewa maso Gabas ko kuma ragowar sassan kasar da ke fuskantar tashi da lafawa na barayin shanu da mutane.

 

Tsallake zuwa bangare na gaba Bincika karin bayani