1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An yanke wa Nnamdi Kanu hukucin daurin rai-da-rai

Abdoulaye Mamane Amadou
November 20, 2025

Shekaru 10 bayan fara shari'ar da ake yi masa bisa zarginsa da yunkurin raba Najeriya, kotu ta kama Nnamdi Kanu jagoran IPOB da aikata laifukan ta'addanci, tare da yanke masa hukucin daurin rai-da-rai.

DW Biafra - Krieg l Nigeria, Nnamdi Kanu vor Gericht
Hoto: Pius Utomi Ekpei/AFP

Masu gabatar da kara sun bukaci a yanke wa Nnamdi Kanu hukuncin kisa, to amma mai shari'a James Omotosho, ya bayyana cewa a yanzu ba a amfani da hukuncin kisa, a maimakon haka ya yanke masa hukuncin daurin rai-da-rai.

 An dai fafata tsakanin jagoran awaren Biafra da kuma wani alkalan da ya yanke hukunci. Su kansu mafi yawan mahalarta zaman shari'ar sun tsorata. Ya dage cewar tada hankalin kadai ne mafita. Wannan barazana ta tada hankali ba komai ba ne face ta‘addanci, da kuma ya aiwatar tare da masu goya masa baya, a cewar mai shari'ar.

Najeriya: Ci gaba da tsare Nnamdi Kanu

Da yake magana a birnin Abuja, alkalin kotun mai shari'a James Omotosho, ya bayyana cewa Nnamdi Kanu, da ya jima yana fafutikar raba Najeriya.To sai dai kuma alkalin da ya dogara a kan wasu faya fayen kalaman Kanun dai, ya tabbatar da laifukan ta‘addanci da tunzura jama‘a ko bayan tsoratarwa da tilasta mutane zaman gida bisa jagoran na aware cikin wasu zarge zarge dai dai har guda bakwai. Tare da tura Kanun zuwa gidan yari har tsawon karshe na rayuwa

Nnamdi KanuHoto: Katrin Gänsler/DW

Yaushe za a shawo kan matsalar tsaron Najeriya?

Shari‘ar Kanun da ke zaman irin ta ta farko da ta kai ga hukuncin mai zafi kan wani dan aware na kasar dai, na zaman zakaran gwajin dafi cikin tarayyar Najeriyar da ke fama da jerin rigingimun rashin tsaron da awaren. A baya dai an kare tare da yafe wa Sunday Igboho da ke neman warewar sashen Kudu maso Yamma, da ma Asari Dokubo da ya jagoranci tunanin ballewar Kudu maso Kudu.

Daga dukkan alamu dai Najeriyar tana da bukatar aiken sako da nufin tunakarar karuwar zubar jini da ake ta'allakawa da batun na ta’addanci, kuma ko bayan Kanun dai ta yi nasarar daure Hussaini ismail da ke zaman jigon ISWAP ta ta’adda ya zuwa shekaru 20 cikin gidan maza.

Masu neman a saki KanuHoto: Tobore Ovuorie/DW

Da ranar yau din ma dai hukumar tsaron farin kaya dai ta sanar da gurfanar da 'ya'yan kungiyar IPOB ta awaren guda Bakwai da suka hada  da Ibrahim Ali Larabo wani dan jamhuriyar Nijar da ke sana’ar canji, kuma ake zargi da samar da kudade ga kungiyar tsagerun IPOB din.

Najeriya: Fara yanke hukunci ga 'yan ta'adda

Nnamdi Kanu, mai shekaru 58 a duniya, ya kokri lauyoyin dake kare shi, ya kuma yi fatali da bukatar lauyan da ya bukaci a bayar da belinsa, ya yi ta hargowa a gaban alkali, har ya kai ga mai shari'ar ya bukaci a fitar masa da shi.

M. Kanu na zama jagoran kungiyar masu ikrarin ballewa daga Najeriya don kafa kasar Biafra  mai 'yanci IPOB, ya share sama da shekaru yana wannan fafutika da ke zama wani babbann zunubi a dokokin kasar ta yankin yammacin Afirka, wacce ta sha da kyar daga yakin basasa na tsawon shekaru.