PDP za ta kori wasu gwamnoni
December 29, 2022Sulhun da aka dauki lokaci ana tunani dai na neman ya gagari masu takama da lemar jam'iyyar PDP Kuma daga dukka na alamu jam'iyyar tana shirin dauka na matakin kora bisa wasu gwamnoninta biyar da suka dauki lokaci suna ja da hukuncin na masu tsintsiyar. Ya zuwa ranar yau dai gwamnonin a karkashin jagorancin gwamnan Rivers Nyesom Wike dai na neman dan takarar da za su goya wa baya da nufin kai wa ya zuwa kirga asara a bangare na uwar jam'iyyar PDP. To sai dai kuma ita ma jam'iyyar ta ce tana tunanin korar gwamnonin dama kwace shugabanci da takararsu a daukaci na jiohohi guda biyar din da suke. Duk wani kokari na yi wa PDP zagon kasa dai a tunanin jam'iyyar na iya kai wa ga hukunci mai tsaurin da ke iya kai wa ya zuwa korar daukaci na gwamnonin daga jam'iyyar ko kuma rushe rassan jam'iyyar a jihohin guda biyar. Duk da cewar dai sai ya zuwa makon gobe ne gwamnonin suka ce za su kai ga yanke hukuncin karshe bisa hanyar da suke shiri da su dauka da nufin samar da makoma.
Ficewar gwamnoni zai kara saka PDP cikin rudani
Duk wani kokari na kauracewa a Atiku a fadar Umar tsauri da ke zaman tsohon sakataren jam'iyyar na kasa, na nufin adabo a cikin inuwar lemar a bangaren gwamnonin. Kashe biri da bindigar igwa ko kuma kokari na kwatar yanci dai daukacin gwamnonin dai na birnin London kuma sun yi wata ganawa da dan takara na jam'iyyar APC, a wani abun da ke nuna alamun rabon kafar tun ba'a kai ga ko'ina ba. To sai dai kuma a yayin da masu tsintssiyar ke kartar kasa bisa makomar gwamnonin dimbi na magoya bayansu dai na fadin da sauran sake cikin tafiyar da ke dada nuna alamun raba kai a tsakanin miliyoyin yayan PDP na kasa. Hashim Suleman dai na zaman mataimaki na shugaban jam'iyyar a Jihar kano daya kuma a cikin masu goya baya ga bangaren na Wike. Ko ya take shirin kayawa a tsakanin masu tunanin Ungulu da ke da kai irin na zabon birni da kuma masu takama da sandar duka dai, da kamar wuya masu takama da lemar gadon, korar gwamnonin guda biyar a tunanin Faruk BB Faruk da ya ce suna da kariyar dokoki na siyasa ta kasar.