Obi zai kalubalanci sakamakon zabe
March 3, 2023Talla
Peter Obi ya bayyana cewar zai shigar da kara a gaban kotu a kan sakamakon zaben da dan takarar jam'iyyar da ke yin mulki Bola Tinubu ya samu nasara. Peter Obi ya bayyana haka ne a lokacin wani taron manema labarai da ya kira: ''Bani ba, ba ku ba, amma al' umma, da yaran da muke rayuwa tare, ina son mutane su fahimci hakan. zan kalubalanci wannan sakamakon zabe wanda aka yi aringinzo kuri'u a ciki. Tun farko dan takarar jam'iyyar adawa ta PDP Atiku Abubakar ya yi korafin cewar an tafka magudi a zaben.