Tasirin sauya sheka a siyasar Najeriya
July 25, 2018Batun na ci gaba da tayar da muhawara a cikin fagen siyasa na kasar a tsakanin masu tunanin makomar siyasa da kuma masu kallon magen lamin da ba ta cizo ba ta kuma yakushi. Duk da cewar, an dade ana ta hasashen yiwuwar tawayen dama yanayin ficewar 'ya'yan jam'iyyar ta APC na ci gaba da daukar hankali a tsakanin 'yan APC mai mulkin dama ita kanta PDP ta adawa.
Har ya zuwa yanzu ba bu tabbaci na rinjaye a tsakanin PDP da ke fadin ta yi sama da kuma APC da ke fadin raunin bai wuci fata ba, daga dukkan alamu dai juyin wainar na shirin barin baya da kura.
Rinjaye a cikin rauni ko kuma kokari na kare sha'awa dai, ana dai kallon sauyin shekar na iya kai wa ga tabbatar da farkon karshe na lafiya cikin majalisar da ta share lokaci tana tangal tangal. Kawo yanzu, shugabannin majalisun guda biyu da suka hada da Bukola Saraki da Yakubu Dogara, ba su baiyana ficewarsu daga APC ba, akwai dai hasashen shugaban kasar zai hango tasku a kokari na amincewa da bukatun mulki a gaba.