1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Najeriya: Rage aikata laifuka ta Intanet

July 17, 2017

Masana ilimin na'urorin sadarwa a Afirka sun bada shawarar matakan rage aikata miyagun laifuka ta hanyar Intanet. Masanan sun ce samar wa matasa masu ilimin na'urorin sadarwa na zamani aiki shi ne mafita.

Kenia Bloggers Association of Kenya
Masana harkokin shafukan Internet a kasar KenyaHoto: DW/J. Mielke

Jami'ar Jos ce ta karbi bakoncin taron masanan da suka fito daga jami'o'in wasu kasashen Afrika, ciki harda Ghana, Saliyo, Gambiya, da kuma Najeriya. Manufar wannan ganawar a cewar Parfessa Tanko Ishaya na jami'ar Jos, ita ce gano yadda ake yawan satar bayanai ta hanyar sadarwar internet a Afrika, da nufin daukan matakai don katse hanzarin masu aikata wannan zalunci.

Masu amfani da shafukan Internet ta wayoyiHoto: Getty Images/AFP/I. Sanogo

Akasarin mukalolin da masana suka gabatar a taron sun fi mayar da hankali ne kan yadda ake samun ci-gaba ta fuskar ilimin na'urorin Comfyuta a Afrika, tare da bukatar samun sauki wajen koyar da dalibai a nahiyar ilimin na'urorin sadarwa na zamani, to sai dai kuma a kasidar da ya gabatar, babban manajan Lardi a hukumar aiwatar da kere-keren na'urorin Komfyuta a Africa Alphi Hamid, ya ce yakamata kungiyar hada kan Afrika ta AU ta yi azamar kafa wata cibiyar sadarwa ta bai daya wacce za ta rika sa ido kan masu aikata zamba ta hanyar sadarwar zamani:

"Ban yi zaton akwai wata hanya guda wacce ta kasance ta tuntuba ce wadda za a rika sadarwa tsakanin kasashen nahiyar Afrika, duk kuwa da irin ci-gaban da ake samu wajen sarrafa na'urori masu kwakwalwa a nahiyar, don haka da yake duniya tana kan ci-gaba, zai da ce kungiyar kasashen Afrika ta AU, ta zaburo don samar da wannan cibiya kuma da kyautata ilimin na'urorin zamani a nahiyar Afrika.”

Amfani da Internet ya zama ruwan dare gama duniya.Hoto: DW/J. Jeffrey

Taron ya kawo shawarar kara ilimantar da jama'a hanyoyin da za a rika amfani da kafar sadarwar ta Internet domin a kasidar da Mohammed kabir Salihu na hukumar NITD da ke Abuja ya gabatar akwai karancin ilimi ga jama'ar da ke amfani da kafar sadarwar Internet a Afrika.  Masana da suka halarci taron sun yi hasashen cewar tare da matakan ci-gaba da ke akwai nan zuwa wasu shekaru kalilan Afirka za ta yi fice tsakanin nahiyoyin duniya wajen ilimin na'urorori masu kwakwalwa.