1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ganawa kan matsalar tsaron Najeriya

June 15, 2020

Gwamnatin Najeriya ta amince da bukatar a sake lale domin shawo kan matsalar tsaron da yankunan arewacin kasar ke fuskanta, inda yanzu 'yan bindiga ke kai hare-hare ba kakkautawa.

Nigeria Präsident Muhammadu Buhari bei Militär in Maiduguri
Hoto: Getty Images/AFP/A. Marte

A yayin da ake ci gaba da kai jerin hare-hare a sassan Arewa maso Gabashin Najeriya ya zuwa yammancin kasar, babban Sufeton 'yan sandan kasar Mohammed Adamu ya ce akwai bukatar sauyi na salo a bangaren  gwamnoni na jihohin a kan hanyar warware matsalar da ke kara kamari. Kama daga Monguno a sashen Arewa Maso Gabas ya zuwa Faskari a sashen yamma dai  an share kusan daukacin makon jiya ana ganin dabam cikin asara ta rayuka da ke ta karuwa sakamakon aiyukan 'yan ina da kisa da kuma masu ta'adda.

Abun kuma da ya tayar da hankalin al'umma na kasa da ke fadin kasa a bangaren na masu mulki na kasar da suka share lokaci suna fadin an kusa karshe amma kuma aka dauki lokacin ana kallon ba daidai. An dai kai har ga wani taron sirri a tsakanin gwamnan Jihar Borno daya daga cikin jihohin da ke ji a jiki da shugaban kasar a wannan Litinin a Abuja, a cikin neman hanyar tunkarar annobar da ke ruruwa irin ta wutar daji yanzu.

Ana ci gaba da tafka asarar rayuka da dukiya a sakamakon aiyukan 'yan bindiga Hoto: AFP/A. Marte

To sai dai kuma babban sufeton 'yan sandan kasar Mohammed Adamu ya ce akwai bukatar sauyi na rawa a bangare na gwamnoni na  jihohin musamman ma na Arewa maso yamman da ke kallon karuwa ta harin. Rashin aikin yi ne dai a fadar Sufeton 'yan sandan ya kai ga karuwar kisan a bangare na masu ta'addan da mafi yawansu ke zaman 'yan kabila ta fulani da kuma ya ce an kwashe musu dukiya a daukaci na jihohin yankin.

Sauyin taku na rawa ko kuma kokari na turin laifi zuwa gaba dai, Abujar da ke kara daukar zafi a cikin gazawar ta tsaro na kuma zargin sarakuna a cikin yankin na arewa da hannu da kafa a cikin abun da ke ta faruwa cikin yankin yanzu. Abun jira a gani dai na zaman yadda take kayawa a kokari na tunkarar annobar da sannu a hankali ke neman janyo bacin 'yan mulki a cikin arewacin kasar da ke zaman tungar goyon baya ga shugaban kasar.