Sultan: Ana rayuwa cikin fargaba a arewacin Najeriya
November 27, 2020Ga dukkan alamu tura ta kai bango kan batun rashin tsaro a tarayyar Najeriya bayan ya dauki hankalin sarakunan kasar irin su Sultan Sa'adu Abubakar da ke zaman sarki mafi tasiri a sashen arewacin Najeriya inda ya ce yankin na Arewa na daukacin mamayar 'yan ina da kisa masu cin karensu ba babbaka.
Karin Bayani: Yawaitar kananan makamai a Najeriya
Sultan Sa'ad ya ce babu kasuwa ba wani kauye da masu aikata ayyukan ta'addanci ba su ratsawa a yankunan arewacin Najeriya, yana mai bayyana irin girman annobar ta 'yan bindiga da kuma kamarin da matsalar tsaro ke kara yi a Najeriya, wacce sarakuna da ma talakawan kasar na yankin Arewa ke cewa hakan na kan hanyar rusa daukacin kasar, a cewar Murtala Aliyu sakataren kungiyar dattawan arewacin Najeriya ACF.
Karin Bayani: Buhari ya magantu kan batun tsaro
Kalaman basaraken na zuwa ne a daidai lokacin da wani rahoto cibiyar kula da ta'addanci ta duniya ke fadin har yanzu Najeriyar na zama ta uku mafi fuskantar annobar 'yan ta'adda a duniya. Kasa da sa'o'i 24 da suka gabata 'yan bindiga sun halaka wani basaraken gargajiya a Jihar Ondo, a ci gaba da hari da satar al'umma da na tabarbarewar tsaro a Arewa maso gabashin Najeriya da ma daukacin sassan arewacin kasar.