1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Najeriya: Rikici ya barke a jamiyyar ADC

Uwais Abubakar Idris
March 16, 2026

Wani rikici ya kuno kai a jamiyyar adawa ta ADC a Najeriya inda wani bangare ya bulla tare da sanar da ranar da zai gudanar da babban taron jamiyyar da ya saba da wanda uwar jamiyyar ta sanar.

Jagoran adawa Atiku Abubakar, Jigo a Jam'iyyar ADC
Jagoran adawa Atiku Abubakar, Jigo a Jam'iyyar ADCHoto: Uwais Abubakar Idris

Wannan takaddama da ta kuno kai a jamiyyar adawar ta ADC a dai dai lokacin da take shirin gudanar da babban taron da ta tsayar za ta gudanar a ranar 14 ga watan Afrilu, ya nuna bullar wani bangare na jamiyyar da ya dade yana ikirarin shine ke da hurumi na jamiyyar ta ADC. Wannan bangaren ya sanar da ranar 3 ga watan Afrilu a matsayin ranar da zai gudanar da babban taronsa. 

Dama jamiyyar adawar ta ADC na fuskantar shari'a a babbar kotun da ke Abuja, inda wasu ke kalubalantar shugabancin Sanata David Mark da Rauf Aregbesola a matsayin shugaba da sakaten jamiyyar. Kotun ta ce kowane bangare ya tsaya inda yake har sai ta yanke hukunci. Wannan sabon bangare na jamiyyar ta ADC da ya fitar da wannan sanarwar ta samu sanya hannun shugaban bangaren jamiyyar Nafiu Bala da sakatarensa Rufus Ikanmi. Alh Nafiu Bala shine shugaban wannan banagare na jamiyyar ta ADC.

Jamiyyun adawar Najeriyar dai sun kasance cikin rigingimu kama daga wacce ke shure-shuren mutuwa sai wacce ba ta da wani tasiri, wannan ya biyo bayan rigingimun da suke fuskanta ne a cikinsu. 

Tuni guguwar siyasar da ke kadawa a Najeriya ta sa 'yan siyasa ke sauya sheka zuwa jamyya mai mulki da ke cika tana batsewa inda wasu yan kasar ke fargabar Najeriyar ta kama hanyar zama kasa mai jamiyya daya tilo.

Tsallake zuwa bangare na gaba Bincika karin bayani

Bincika karin bayani