1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Rohoto kan yaki da cin hanci a Najeriya

Uwais Abubakar Idris SB/LMJ
January 30, 2024

Najeriya ta samu ci gaba da matakai biyar a raguwar yaki da cin hanci da rashawa da Transparency International da ke yaki da cin hanci ta kadammar a Talata. Rahotonta na 2023 in aka kwatanta da matsayin kasar a baya.

Transparency International Logo
Hoto: Rafael Henrique/ZUMA Wire/IMAGO

Najeriya ta samu ci gaba da matakai biyar a raguwar yaki da cin hanci da rashawa da kungiyar Transparency International da ke yaki da cin hanci ta kadammar a Talatar nan. An samu ci gaban ne a rahotonta na 2023 in aka kwatanta da matsayin Najeriya a shekarun baya.

Karin Bayani: Bincike a kan wata minista a Najeriya bisa zargin cin hanci

Rahoton cin hanci game da kasashe

Wannan ne karon farko a ‘yan shekarun nan da Najeriya ta samu ci gaba a fanin yaki da cin hanci da rashawa a rahotanin da kungiyar ta Transparency ke fitarwa kowace shekara. Domin rahoton ya nuna cewa Najeriyar ta matsa daga mataki na 150 a cikin kasashe 180 a duniya zuwa mataki na 145. To sai dai maki 25 ta samu a cikin 100 domin ta matsa ne daga matsayi 24 da ta samu a 2022 zuwa na 25. Sin wannan za a ce nasara ce ko kuwa dai irin na mai ginin rijiya ne? Mallam Auwal Musa Rafsanjani shi ne wakilin kungiyar Transparency a Najeriya kuma shugaban kungiyar Cislac da suka hada gwiwa wajen kadammar da rahoton, wanda yake ganin abubuwa da dama suka janyo wannan sakamakon.

Rahoton kungiyar na wannan shekara ya gano yadda matsaloli na cin hanci da rashawa ya kazanta a kasar, kama daga sashin shari'a na alkalai da ‘yan siyasa da ma fanin tsaro duk kanwar ja ce, ture kaza kwashe kwai ake yi a yanayin da ke haifar da koma bayan da ake fuskanta.

Zanen barkwanci

A watan Mayun 2023 Najeriya ta kadammar da rajistar bayyana su wanene ke da malakar kadarori a kamfanoni a kasar wanda duk wanda keda kasha biyar sai sunasa ya bayyana. Tuni gwamnatin Najeriya ke murna da wannan ci gaba, kungiyoyin yaki da cinci da rashawa na Najeriya sun ba da shawara ga gwamnatin kasar a kan hanyoyin da ya kamata a bi wajen rage wannan matsala.

Mallam Auwal Musa Rafsanjani ya bayyana hatsarin da ke fuskantar Najeriya muddin ta ci gaba da bari matsalar cin hanci da rashawa na karuwa a cikin al'umma ba tare da daukan matakin da ya dace ba. Rahoton da kungiyar ta Transparency International ke fitarwa shine mafi inganci da ake amfani da shi a duniya wajen auna mizanin cin hanci da rashawa a kowace kasa ta duniya.