1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Najeriya: Rufe filin jirgin sama na Abuja

Lateefa Mustapha Ja'afar
March 9, 2017

Najeriya: Ra'ayoyi sun banbanta sakamakon karkatar da akalar jigilar jiragen sama daga filin jirgin sama na Abuja zuwa na jihar Kaduna.

Gyaran filin jirgin sama na Abuja da mayar da jigilar jiragen zuwa Kaduna
Gyaran filin jirgin sama na Abuja da mayar da jigilar jiragen zuwa Kaduna

A Najeriya ra'ayoyi sun ban-banta dangane da batun yin gyara a filin sauka da tashin jiragen sama na Abuja, inda a yanzu haka aka rufe filin tare kuma da karkatar da akalar jiragen da ke hada-hada a cikinsa zuwa jihar Kaduna da ke makwabtaka, har nan da tsahon makwanni shida masu zuwa.