1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ko an hana 'yancin albarkacin baki a Najeriya?

August 21, 2025

Wani rahoto na Hukumar Kula da Fasahar Kafafen Sada Zumunta na Zamani a Najeriya, ya ce a shekarar da ta gabata gwamnatin kasar ta rufe kafafen kusan miliyan 20 a kasar.

Najeriya | Shugaban Kasa | Bola Ahmed Tinubu | Rufewa | Kafofin Sada Zumunta
Shugaban Najeriya Bola Ahmed TinubuHoto: Sarah Meyssonnier/Pool Photo via AP/picture alliance

Hukumar Kula da Fasahar Kafafen Sada Zumunta na Zamani a Najeriyar ta ce, mafi yawan kafafen da aka rufe din sun hadar da na masu cin-zarafin kananan yara da masu tsorata jama'a da yada bayanan tsana da ma kafafen karya. Da ma dai an dauki lokaci ana kai-kawo cikin kasar, a kokarin masu mulkin Najeriyar na jan ragamar harkokin kafofin sada zumuntar da ke kasar. Kafin wata sabuwar sanarwar da a cikinta gwamnatin tarayyar ta ce ta soke kimanin kafofin sada zumunta miliyan 19 da dubu 500.

Karin Bayani: Cin zarafi ta kafofin sadarwa na sada zumunta

Babbar hujja dai a fadar wani rahoto na hukumar da ke kula da fasahar ta zamani, na zaman cin zarafin yara da masu nuna batsa ko bayan kafofin da ke yin barazana ga rayuwar 'yan Najeriya. Sanarwar dai ta ce kafofin TikTok miliyan biyu da dubu300 ne hukumar ta ce an toshe sakamakon laifuka dabam-dabam, a yayin da kuma hukumar ta tsayar da ayyukan kafofin LinkedIn miliyan 16. Shi ma dai kamfanin Google ya toshe kafofi sama da dubu 900 da ke taka rawa a karkashin kafofin zumuntarsa, duk ya zuwa karshen shekarar da ta shude.

Najeriya: Malamar da ke koyar da Fulatanci

03:08

This browser does not support the video element.

Duk da cewar dai Najeriyar ta dade tana ji a jiki, sakamkon rawar kafofin sadarwa na zamanin, matakin na Abuja da ke zaman irinsa na farko na janyo dagun hakarkari cikin kasar a halin yanzu. Kokarin kare hakki ko kuma neman kare rayuwa a jihohi dabam-dabam na kasar, ana ganin karuwar cin-zarafin masu sukar gwamnoni a kafafen na zumunta. To sai dai kuma, barazanar ba ta kai cikin gidan masu jaridun Najeriyar ba da ke fadin gwamnatin tana bisa daidai. Ya zuwa yanzun dai Najeriyar na kallon karuwa ta laifuka cikin kafafe na zumuntar, kuma bankuna da tajirai ciki da ma wajen kasar dai na ji a jiki daga masu amfani da kafafen da nufin laifukan kudi.

Karin Bayani: Takaddama kan rufe kafofin yada labarai

To sai dai kuma akwai tsoron yin kai mai uwa da wabi cikin matakin na Abuja da ko bayan masu laifuka, yana iya shafar ragowar jama'ar cikin gari da ba su da laifi. Barrister Muhammed Tudun Wada dai na zaman shugaban kungiyar lauyoyi Musulmi na kasar, kuma ya ce hakkin da ke cikin kasar a kafafen na zumunta mai linzami ne. Ya zuwa yanzun dai Tarayyar Najeriyar na tsakanin wankin suna da kila ma kimarta cikin idanun duniya da kuma dakile hakkin 'yan kasar, cikin batun 'yancin fadar albarkacin baki mai tasiri cikin dimukuradiyyar Najeriyar.