1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Coronavirus: Rudani a majalisar Najeriya

Uwais Abubakar Idris LMJ
March 4, 2020

Majalisar wakilan Najeriya ta janye batun rufe majalisar kasar da a baya ta ce za ta yi, sakamakon samun mutum guda da ke dauke da kwayar cutar Coronavirus ko COVID-19 a kasar.

Nigeria National Assembly
'Yan majalisar wakilan Najeriya sun jingine kudirin dage zamansua sabo da CoronavirusHoto: Nigeria Office of the House of Representatives

Tun dai a Litinin din wannan makon ne majalisar wakilan Najeriyar ta tafka muhawara tare da yanke shawarar dakatar da harkokinta da ma rufe majalisar baki daya har tsawon makonni biyu, sakamakon kudirin gaggawa da dan majalisa Ndidi Elumelu ya gabatar gabanta na bukatar a dakatar da harkokin majalisar sakamakon bullar cutar Coronavirus ko kuma COBID 19 a kasar. Majalisar dai ta karbi kudirin hannu biyu, inda ta ce za ta dage zamanta kasancewar mutum bai san da wanda zai gaisa ba, abin da zai iya kara yaduwar cutar. Al'ummar Najeriyar dai sun mayar da martani mai zafi, ganin cewa mutum guda ne kacal aka gano yana dauke da kwayar cutar ta Corona, abin da kuma za a iya cewa ya tilastawa majalisar wakilan dakatar da kudirin dage zaman nata, abin kuma da ya dauki hankali ganin cewa a baya mjalisar na yin uwa ta yi makarbiya kan al'amuran da suka shafe ta ba tare da damuawa da wani matsin lamba daga al'ummar kasar da ma kungiyoyin fararen hula ba.