Za a rufe makarantun tsangaya a Najeriya
April 22, 2020![children beggers](https://static.dw.com/image/1746120_800.webp)
Talla
Gwamnonin sun yanke wannan shawarar ce ganin yadda almajirai ke tattare da hadarin kamuwa da cutar COVID 19.
Za a rufe makarantun sannan za a mayar da yaran ga iyayensu ko kuma jihohin da suka fito, a yayin da yaran da suka kasance marayu za a barsu a jihohin da suke karkashin kulawsar gwamnatin jihar.
Kungiyar hakkin musulmi MURIC ta kiyasta cewa akwai yara almajirai sama da yara miliyan goma a Najeriya.