1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Najeriya: Sabon haraji kan man fetur da Gas

Uwais Abubakar Idris
October 31, 2025

Wata takadama ta kuno kai bayan bullo da harajin kashi 15 cikin dari da gwamnatin Najeriya ta yi a kan masu shigowa da man fetur da diesel cikin kasar,

Gidan man NNPC a Abuja-Nigeria
Gidan man NNPC a Abuja-NigeriaHoto: AFOLABI SOTUNDE/REUTERS

Sanya wannan sabon haraji na kashi 15 cikin 100 a kan man fetur da na diesel da ake shigowa da shi Najeriya, wani mataki ne na kara mayar da fanin albarkatun man fetur a hannun ‘yan kasuwa zalla, tare da tsame hannun gwamnati, kasuwa ta yi halinta. Matakin ya biyo bayan ci gaba da shigo da man da wasu ‘yan kasuwa ke yi duk da cewa Najeriyar na da matatar mai ta Dangote wacce har ta kai ga ga fitar da tattacen mai zuwa kasashen ketare. Ko mecece hikimar daukar wannan mataki ga Najeriyar da ke sa ran samun karin kudadden shigar da za su zarta Naira tirliyan hudu?  

Najeriyar dai na kara daukar sabbin matakai da ke zamanatar da harkar man fetur na kasar. Ana kalon bullo da haraji a kan man fetur da iskar gas a matsayin hanyoyin kare masana'antu na cikin gida don a daina shigo da man fetiu din daga kasashen waje da ya kai ga zame wa Najeriya abin kunya. Ta kai ga wasu ‘yan kasuwa sun yi kememe sun ki sayen man fetur daga matatar Dangote suna shgowa da shi kasar, yayin da matatar ke fitar da shi zuwa kasashen waje. 

Tuni wasu masu hada-hadar man fetur din suka fara nuna damuwa ko wannan zai haifar da karancin man fetur a Najeriyar saboda tunanin fuskantar karancinsa, ko kuwa an yi ne don hana wasu yan kasuwar da buda wa Dangote kafar yin babakere. Matatar mai ta Dangiote dai na samar da ganga dubu 650 a kowace rana sannan akwai shirin fadada wannan zuwa ganga milyan 1.4 wanda ya zarta yawan man da Najeriya ke amfani da shin na lita milyan 50 a kowace rana. 

Kwararru na fatar cewa a yadda ake tafiya Najeriyar za ta iya komawa shekarun baya da bata shigo da tattacen mai sai dai fitar da shi zuwa kasashen waje, musamman idan gwamnati ta gyara matatun da take da su guda hudu a kasar.

Tsallake zuwa bangare na gaba Bincika karin bayani

Bincika karin bayani