Yara sun halaka a wani hari a Najeriya
January 31, 2020
Talla
Rahotanni sun nunar da cewa yarinyar mai kimanin shekaru 12, ta tayar da bam din da ke jikintan ne, a wata Islamiyya da ke garin Muna Dalti da ke wajen birnin Maiduguri fadar gwamnatin jihar Bornon Najeriyar, a daren Alhamis din da ta gabata. Kawo yanzu dai babu wata kungiya da ta dauki alhakin harin, sai dai kungiyar Boko Haram da ta addabi Najeriyar da makwabtanta, na ci gaba da zafafa hare-hare a wannan yanki, duk kuwa da ikirarin da mahukuntan kasar ke iy na cewa sun karya lagonta.