1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Cece-kuce kan sabon shugabanci a APC

March 8, 2022

Kasa da makonni uku a gudanar da babban taron jam'iyyar APC mai mulki a Najeriya, batun sabon shugabanci ya janyo cece-kuce da ma rashin tabbas.

Najeriya I APC
Jam'iyyar APC mai mulki a Najeriya na cikin halin taskuHoto: DW/K. Gänsler

Duk da cewar jam'iyyar na da alamun zamowa dashi mai rai guda tara, sabon sauyin shugabancin a APC ya girgiza masu tsintsiyar da ma 'yan kallo a daukacin Tarayyar Najeriyar. Sau dai-dai har kusan uku ne dai tsohon shugaban jam'iyyar na kasa Mai Mala Buni ke daga babban taron jam'iyyar na kasa, kuma sau ukun yana shanyewa kafin sabon matakin da har yanzu 'yan kasar ke neman amsarsa. To sai dai kuma maye gurbin gwamnan Yoben da dan uwansa na Niger Abubakar Sani Bello dai, na nuna irin girman rikicin da ke cikin gwagwarmayar neman magajin shugaban kasar a zabe na badi. Duk da cewar dai Buni da ke jinya a kasar Dubai a halin yanzu, bai ce komai a cikin juyin mulkin da ke da goyon bayan fadar gwamnatin kasar ba da kamar wuya ace anzo karshen rikicin cikin gidan APC da ke fuskantar zabuka iri-iri a lokaci kankane. Cikin kasa da makonni uku masu tsintsiyar suka tsara samar da shugabancin jam'iyyar a mataki na kasa, shugabancin kuma da suke fatan zai kai ga samar da dan takarar shugabancin kasar a kasa da watanni hudun da ke tafe.

Ba wai uwar jam'iyyar ce kawai ke fama da rikicin cikin gidan ba, har ma da jihohi

Abun kuma da ya kara fito da jan aikin da ke gaban sabon shugaban da ya hau ragamar ikon jam'iyyar cikin tsakiyar rabuwar kawuna fili. Akwai dai tsoron sabon shugabancin APC ka iya komawa ya zuwa dan raka gawa, maimakon mai ceton rai na masu tsintsiyar a halin yanzu. To sai dai kuma a fadar Faruk BB Faruk da ke sharhi kan al'amuran siyasa na kasar, jam'iyyun Najeriyar ba sa mutuwa irin ta COVID-19. Duk da cewar dai ana yi wa sabon shugaban kallon dan ba ruwanmu cikin rikicin APC da kamar wuya ya iya shawokan manyan jiga-jigan jam'iyyar da kansu ke rabe. Burin mulkin ne dai ya kai Buni  jan kafa ga kai wa ya zuwa babban taron, kuma burin mulkin ne daga dukkan alamu ya kai ga kare masa mulkin na shekaru kusan biyu. A cewar Isa Tafida Mafindi da ke zaman jigo a jam'iyyar ta APC, zai wahala sabon shugabancin ya kawo sauyin da masu tsitsiyar ke fatan gani ido rufe cikin jam'iyyar. Abun jira a gani dai na zaman yadda take shirin kayawa, a tsakanin shugaban kasar da ke nuna alamun gajiyawar da gwamnonin da ke dada nuna alamun karfi na tsiya a cikin jam'iyyar.