1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kokarin hana cin-zarafi a jami'o'in Najeriya

Uwais Abubakar Idris LMJ
November 6, 2025

Majalisar dattawan Najeriya ta amince da daurin shekaru 14 a kan duk wanda aka samu da laifin cin-zarafin daliban jami'o'i da sauran manyan makarantu a kasar.

Najeriya | Majalisar Dattawa | Doka | Cin-zarafi | Dalibai | Jami'o'i
Majalisar dattawan Najeriya ta amince da tsaurara hukunci kan cin-zarafin daliban jami'o'i Hoto: Wang Guansen/Xinhua/picture alliance

An dai tanadi hukunci mai tsaurin gaske, domin dakile matsalar ta cin-zarafin dalibai a manyan makarantun Najeriyar musamman ma dai 'yan mata da malamansu ke fusknatar zargin yin lalata da su kafin su samu nasara a jarrabawa. Sanata Oyelola Ashiru shi ne mataimakin shugaban masu rinjaye a majalisar dattawan da ya gabatar da kudurin dokar da majalisar ta amince da ita, kuma a cewarsa: "Kokari ne na kare martabar dalibai a dangantakarsu da mallamai a manyana makarantu da ake da su a kasar."

Wannan kudurin dokar ya ayyana cewa duk wata magana ta yi wa 'yan mata kwarkwasa da furta kalamai na nuna aniyar cin-zarafinsu, ko runguma da sumbata a tsakanin masu bayar da ilimi ga dalibai maza da mata laifi ne. An tsara hukuncin da ya kama daga shekaru biyar har zuwa 14 a gidan yari, ba tare da zabin biyan tara ba. Tuni kungiyoyin da ke fafautukar kare cin-zarafin mata suka fara mayar da martani.

Magance matsalar fyade Katsinan Najeriya

03:02

This browser does not support the video element.

Kungiyara kare hakin dan Adam ta kasa da kasa Amnesty International, na cikin wadanda suka yi ta gangami da matsin lambar ganin an samu samar da dokar. Wani muhimmin sashe na kudurin dokar shi ne, tanadin cewa laifi ne ga duk jami'ar da ta ki sanar da aikata laifin cin-zarafin dalibai ko ta yi kokarin yin rufa-rufa.

An kara tsananta hukuncin da nufin dakile matsalar, saboda yadda take neman zama ruwan dare. Kwararru na bayyana cewa fitowa fili a bayyana laifin, zai taimaka sosai. Akwai 'yan majalisar da suka nuna bukatar a sake fadada dokar ta shafi sauran al'umma, ba kawai dalibai ba.

Tsallake zuwa bangare na gaba Bincika karin bayani