Jam'iyyu 70 sun sa hannu a daftarin zaman lafiya
February 13, 2019Talla
A gaban manyan 'yan kallon cikin gida da ma waje ne dai manya da kanana na masu takara ta shugaban kasa suka rattaba hannu a bisa wata sabuwar yarjejen iyar dake zaman ta biyu cikin tsawon wata biyu.
Yarjejeniyar dai ta tanadi kaiwa ga gudanar da zabukan cikin zaman a lafiya da kuma karbar sakamako bayan tabbatar da shi.
Kuma kama daga shi kansa shugaban kasar ya zuwa ga madugun adawa ta kasar dai daya bayan daya a cikin masu takarar sama da 70 suka rika rattaba hannun amincewa da yarjejeniyar da ke zaman gada a tsakanin kasar da fadawa rudani.
Akwai dai alamun dardar tun daga kalaman manyan jam'iyyun kasar guda biyu da kuma yadda magoya bayan jam'iyyun suka rika kai hari a kan abokai na hammaya a kwanakin dake gabatar zaben.