1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Najeriya: Samar da tsaro a tsakanin Abuja da Kaduna

June 14, 2017

Rundunar 'yan sandar Nigeria ta jibge jami’an tsaro 600 akan hanyar Abuja zuwa kaduna, sakamakon karuwar ayyukan masu garkuwa da mutane da ‘yan fashi da makami da suka addabi jama'a.

Bombenexplosion Polizei in Nigeria
Manyan jami'an tsaron 'yan sanda a NajeriyaHoto: picture-alliance/AP Photo

Wannan dai shi ne karo na farko da rundunar ‘yan sandar Najeriya ta dauki matakan Jigbe jami'an tsaro na musanman da ke da yawan mutun 600 akan haryan kaduna zuwa Abuja. Kuma shirin an kaddamar da shi ne a wani kauyen Rijana da ke a karamar hukumar Kachia wanda ke a yankin kudancin Kaduna tare da halartan manyan shugabannin ‘yan sanda daga sassa daban-daban na fadin kasar dan tunkarar wannan kalubalen da ke janyo komabaya ga harkar bunkasa tattalin arziki da zirga-zirgan jama'a.

DIG Habila Joshak shi ne dai mukaddashin shugaban ‘yan sandan Nigeria da ya wakilci shugaban ‘yan sanda kasar AIG Ibrahim Idris wajen kaddamar da shirin "Special intervention force” domin aikawa da wadannan jami'an tsaron hanyar Abuja dan bayar da kariya ga matafiya tare da ceto wadanda aka yi garkuwa da su dan neman kudin fansa:

Samar da tsaro tare da ban-hannun jama'a

'Yan sanda masu kwantar da tarzoma a NajeriyaHoto: imago/Xinhua

"Guda dari biyar daga cikin su dai 'yan sanda ne zalla, sannan kuma saura wasu guda dari ‘yan sandan farin kaya ne, wadanda aka sanya su zama a cikin shirin ko ta kwana akan hanyar, domin magance matsalar sace-sace da garkuwa da mutane matafiya da 'yan fashi da makami da sauran miyagun mutane ke gudanarwa a kan hanyar. A wannan shirin da muka kaddamar a yau, muna fatan cewa zai bayar da dama ta samar da isashen tsaron da ake bukata, wanda kuma zai kare rayuwar dukkanin matafiya da dukiyoyinsu tare kuma da tabbatar da ganin cewa an shamo bakin zaren wannan matsalar ta yin garkuwa da matafiya da ta sake dawowa a wannan yankin."

DIG Habila, ya kuma kara da cewa aikin ‘yan sanda ne na tabbatar da tsaro a ko'ina a cikin kasa tare da kare dukiyoyin jama'a saboda haka su na fatan samun hadin kan da suke bukata daga bangaren al'ummar kasa na tallafa wa jami'an tsaro da dukkanin bayanan da suka bukata, domin dakile munanan ayyukan miyagun mutane da ke garkuwa ko sace matafiya a kan hanyarsu. Ruta Samuel wata yarince wadda ta kwashe kwanaki biyar a hannu wadanda suka yi garkuwa da ita a cikin daji, ta bayyana cewa akwai mutane da yawan gaske da yanzu haka aka yi garkuwa da su a cikin dajin.

Shugaban 'yan sandan jihar Lagos Abayomi ShogunleHoto: DW/A.Kriesch

Kwato wadanda aka yi garguwa da su da kuma hana yin garkuwa

"Akwai mutane dayawa da aka sace da suke cikin wannan daji, kuma masu garkuwa da mutanen su na yin lalata da mata, tare kuma kashe wadanda suka kasa biyan kudaden da ake so su bayar, ta ce akwai bukatar ceto wadanda ke a hannun wadannan mutane tun kamin su hallaka su."

Masana harkokin tsaro na ganin cewa tun bayan dakatar da ayyukan sufurin jirgin sama daga Kaduna zuwa Abuja ne wannan matsala ta sake dawuwa sakamakon kwashe jami'an tsaro da ke bisa wannan hanya. Sai dai yanzu ‘yan sanda da aka kawo wadanda suka kware ne a harkar yaki da ayyukan ‘ta'addanci da kuma samar da bayanai kan harkokin tsaro, wadanda yanzu haka aka soma rarraba su a wurare daban-daban domin soma gudanar da ayyukan.